Na yarda da kayen da Atiku ya yi mana, kuma zan taya shi kamfen - Jang

Na yarda da kayen da Atiku ya yi mana, kuma zan taya shi kamfen - Jang

Daya daga cikin ‘yan takarar shugabancin kasar nan a karkashin jam’iyyar PDP, Jonah Jang, ya taya Atiku Abubakar murna a kan nasarar da ya samu a kan su. Sannnan kuma ya yi alkawin goya masa baya har ya samu nasara.

Jang ya yi wannan sanarwar taya murna da alkawarin goyon baya ne a cikin wata takarda da ya raba wa manema labarai, a Jos, Babban birnin jihar Plateau.

Jang, wanda ya zo na biyun na karshe da kuri’u 19, ya bayyana Atiku a matsayin shugaban da ke jira kawai a rantsar da shi.

Na yarda da kayen da Atiku ya yi mana, kuma zan taya shi kamfen - Jang

Na yarda da kayen da Atiku ya yi mana, kuma zan taya shi kamfen - Jang
Source: Depositphotos

Daga nan sai ya roke shi da cewa idan ya yi nasara to ya duba abubuwan da ke damun yankin Arewa ta Tsakiya.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa bayan bayyanar tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, a matsayin dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), kungiyar shugabannin Yarbawa, Afenifere tace zata zauna don yanke shawarar wanda zata zaba a matsayin shugaban kasa.

KU KARANTA KUMA: 2019: ADC ta zabi tsohon mataimakin shugaban banki CBN a matsayin dan takarar shugaban kasa

Kungiyar da farko wacce ta karbi bakuncin Atiku a Akure, babban birnin jihar Ondo tayi alkawarin zabar duk dan takarar da ya amince da sauya fasalin lamuran kasar.

Da yake magana da majiyarmu a Akure a ranar Lahadi kan lamarin, babban sakataren kungiyar Afenifere, Bashorun Sehinde Arogbofa ya bayyana Atiku a matsayin dan siyasar da ya biya diyarsa a siyasar Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel