Tunde Bakare ya nemi Buhari ya kira taron kasa

Tunde Bakare ya nemi Buhari ya kira taron kasa

Babban Fasto kuma dan siyasa, Tunde Bakare, ya yi kira ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya yi gaggawan yin amfani da karfin ikon sa, ya kira taron gaggawa kan Makomar Kasar domin a tattauna yadda za’a wanzar da zaman lafiya tare da juna.

Ya kuma yi kira ga sauya fasalin lamuran kasar domin ta koma kamar yadda take a baya wato tsintsiya madaurinki daya.

Bakare wanda a zaben 2011 shi ne ya fito ma matsayin mataimakin Muhammadu Buhari a karkashin CPC, ya bayyana haka kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa, NAN ya ruwaito, a Ikeja, a wani taron manema labarai.

Ya ce ya yi wannan kira ne duba ga yadda manyan masu tofa albarkacin bakin su dangane da inda Najeriya ta dosa, ke ta kumajin cewa lokaci ya yi da za a kira taron makomar kasar nan.

Tunde Bakare ya nemi Buhari ya kira taron kasa

Tunde Bakare ya nemi Buhari ya kira taron kasa
Source: Depositphotos

Ya ce haka ne zai kara dankon hadin kai, tabbatar da zaman lafiya, ci gaba da kuma shimfida adalci a kan abububan da suka jibinci kason arzikin kasar nan.

Bakare ya kara da cewa Buhari ya tuntubi Majalisar Tarayya da ta Dattawa da kuma Majalisar Zartaswar kowace jiha, ta yadda zai kafa kwamiti na shugaban kasa da zai ja ragamar gudanar da taron makomar kasar.

KU KARANTA KUMA: Za mu yanke shawarar bayan wanda za mu bi tsakanin Buhari da Atiku - Afenifere

A karshe ya ce Buhari ya yi kokari ya dora jan namijin da ba shi da ganin kyashi, mai kishi kasar nan, ba kishin bangaranci ba, kuma mai jaddada adalci wanda zai ja ragamar sake dinkewar kasar nan daram dam-dam, daga irin zaman doya-da-manjan da ake yi yanzu tsakanin wannan yanki da wancan.

Ya ce mai kishin da kudi ba za su iya rufe masa ido ba ne ya kamata a dora a kan wannan mukami.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel