Majalisar Koli ta Musulunci ta bukaci a hukunta masu hannu a kashe-kashen Plateau

Majalisar Koli ta Musulunci ta bukaci a hukunta masu hannu a kashe-kashen Plateau

Majalisar Koli ta Harkokin Musulunci a Najeriya, ta yi Alla-wadai da kisan kiyashin da ya sake kunno kai a jihar Plateau kwanan nan.

A cewar wata takarda daga Majalisar dauke da sa hannun mataimakin babban sakatare ta, Salisu Shehu, majalisar ta yi kira da a gaggauta kamo masu hannu a kisan sannan kuma ta bukaci a hukunta su.

Majalisar ta nuna bakin ciki kan yadda jihar Filato a baya ta ke a matsayin cibiyar zangon zaman lafiya, amma yanzu jihar ta munana da kakshe-kashen kabilanci da addinanci, musammman a kananan hukumomi uku, da suka hada da Barkin Ladi, Riyom da kuma Jos ta Kudu.

Majalisar Koli ta Musulunci ta bukaci a hukunta masu hannu a kashe-kashen Plateau

Majalisar Koli ta Musulunci ta bukaci a hukunta masu hannu a kashe-kashen Plateau
Source: Depositphotos

Ta bayyana kabilar Kiristocin Birom da cewa su ne manyan ‘yan ta’addan da ke yi wa jama’a kisan kiyashi ta hanyar danne sauran kabilu, musamman Musulmai, yadda abin ya kai har su ka tare musulmai su ka kone su, su na cin naman jikin su a lokutan shagulgulan musulmai.

A karshe Majalisar ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta dora laifin kisan Janar Alkali da sauran musulmai da aka kashe a kan kabilar Birom da ke yankin.

KU KARANTA KUMA: Za mu yanke shawarar bayan wanda za mu bi tsakanin Buhari da Atiku - Afenifere

Majalisar ta yaba da kokarin da Gwamna Simon Lalong ke yi na tabbatar da zaman lafiya a jihar.

Ta kuma soki wasu kafafen yada labarai da kira na kudancin kasar nan wadanda suke rufe ido, su ke jin kunyar buga mummunar barnar da ake yi wa Musulmai a Filato, musamman rashin bada fifiko wajen batun kisan Janar Idris Alkali.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel