Gwamna Yari ya gudanar da zaben fitar da gwani cikin dare

Gwamna Yari ya gudanar da zaben fitar da gwani cikin dare

Ana saura awa hudu da lokacin da hukumar gudanar da zabe na kasa mai zaman kanta wato INEC ta bada na kulle kofan zaben fitar da gwani, gwamnan jihar Zamfara, AbdulAziz Yari ya bada umurnin gudanar da zaben cikin dare.

Gwamnan ya jaddada cewa ba zai taba yarda yan adawansa na cikin gida su samu nasara a wannan zaben ba.

Gwamna Yari ya gudanar da zaben fitar da gwani cikin dare

Gwamna Yari ya gudanar da zaben fitar da gwani cikin dare
Source: Depositphotos

A jiya Lahadi, 7 ga watan Oktoba, 2018 mambobin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Zamfara sun baiwa hammata iska wajen ganawar masu ruwa da tsaki kan zaben fidda gwanin gwamna da yan majalisan dokokin tarayya.

KU KARANTA: Hukumar DSS ta garkame Sanata Kabiru Marafa

Gwamnan jihar ya sanar da cewa lallai za’a gudanar zaben fidda gwanin gwamna, majalisar dokokin tarayya da jiha daga karfe takwas na dare a fadin jihar kuma za’a sanar da sakamakon kafin gari ya waye, amma har yanzu shiru.

Jaridar Leadership ta bada rahoton cewa diraktan DSS na jihar Zamfara ya umurci jami’ansa su tafi da Sanata Marafa amma dogaransa suka ki, daga baya, Marafa ya amince da binus ofishin DSS.

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa damu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel