Shugabancin kasa: Atiku na mafarki ne kawai – Lauretta Onochie

Shugabancin kasa: Atiku na mafarki ne kawai – Lauretta Onochie

- Lauretta Onochie, hadimar Shugaban kasa Muhammadu Buhari na musamman a kafofin watsa labarai ta caccaki Alhaji Atiku Abubakar

- Tace lashe tikitin da Atiku yayi zai ba APC sa'a cikin sauki

- Onochie tace sai da Atiku siya sannan ya iya ja da abokan takararsa

Lauretta Onochie, hadimar Shugaban kasa Muhammadu Buhari na musamman a kafofin watsa labarai ta caccaki Alhaji Atiku Abubakar, bayan ya billo a matsayin wanda zai tsayawa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) takara a zabe mai zuwa.

Ta je shafin zumunta, jim kadan bayan kaddamar da sakamakon cewa Atiku ne yayi nasarar samun tikitin takarar jam’iyyar cewa hakan zai basu dama cikin sauki, jaridar Punch ta ruwaito.

Shugabancin kasa: Atiku na mafarki ne kawai – Lauretta Onochie

Shugabancin kasa: Atiku na mafarki ne kawai – Lauretta Onochie
Source: Depositphotos

Legit.ng ta tattaro cewa hadimar shugaban kasar tayi ikirarin cewa Atiku ya gudu daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) don guje ma karawa da Buhari a zaben fidda gwani; sannan cewa tsohon mataimakin shugaban kasar yayi gwagwarmayan kafin ya samu tikitin jam’iyyar.

KU KARANTA KUMA: Muhimman abubuwa 5 da Atiku ya fadi a jawabinsa na lashe zaben cikin gida na PDP

A baya Legit.ng ta rahoto cewa kungiyar shugabannin Yarbawa, Afenifere tace zata zauna don yanke shawarar wanda zata zaba a matsayin shugaban kasa.

Kungiyar da farko wacce ta karbi bakuncin Atiku a Akure, babban birnin jihar Ondo tayi alkawarin zabar duk dan takarar da ya amince da sauya fasalin lamuran kasar.

Da yake magana da majiyarmu a Akure a ranar Lahadi kan lamarin, babban sakataren kungiyar Afenifere, Bashorun Sehinde Arogbofa ya bayyana Atiku a matsayin dan siyasar da ya biya diyarsa a siyasar Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel