Za mu yanke shawarar bayan wanda za mu bi tsakanin Buhari da Atiku - Afenifere

Za mu yanke shawarar bayan wanda za mu bi tsakanin Buhari da Atiku - Afenifere

- Kungiyar shugabannin Yarbawa, Afenifere tace zata zauna don yanke shawarar wanda zata zaba a matsayin shugaban kasa

- Tayi alkawarin zabar duk dan takarar da ya amince da sauya fasalin lamuran kasar

- Sakataren kungiyar yace ya zama dole masu adawa su hada kansu don tsige jam’iyya mai mulki a zabe mai zuwa

Bayan bayyanar tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, a matsayin dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), kungiyar shugabannin Yarbawa, Afenifere tace zata zauna don yanke shawarar wanda zata zaba a matsayin shugaban kasa.

Za mu yanke shawarar bayan wanda za mu bi tsakanin Buhari da Atiku - Afenifere

Za mu yanke shawarar bayan wanda za mu bi tsakanin Buhari da Atiku - Afenifere
Source: Depositphotos

Kungiyar da farko wacce ta karbi bakuncin Atiku a Akure, babban birnin jihar Ondo tayi alkawarin zabar duk dan takarar da ya amince da sauya fasalin lamuran kasar.

Da yake magana da majiyarmu a Akure a ranar Lahadi kan lamarin, babban sakataren kungiyar Afenifere, Bashorun Sehinde Arogbofa ya bayyana Atiku a matsayin dan siyasar da ya biya diyarsa a siyasar Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Marafa yayi wa Gwamna Yari wankin babban bargo akan zaben fidda gwani a Zamfara

Ya kuma bayyana cewa ya zama dole masu adawa su hada kansu don tsige jam’iyya mai mulki a zabe mai zuwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel