An kama limamai da suka kasa tayar da matacce bayan sunce za su iya

An kama limamai da suka kasa tayar da matacce bayan sunce za su iya

- Wata mace mai suna Asineyi Biira ta shiga cikin dimuya da damuwa bayan jaririnta ya mutu a hannun Fasto

- Jaririn na fama da rashin lafiya ne sai Fasto, Viola Nassanga ta shawarci Biira ta kawo shi domin ayi masa addu'a

- Daga baya, jaririn ya mutu a hannun Fasto kuma tayi ikirarin za ta dawo masa da ransa amma hakan bai yiwu ba

- Rashin iya dawo da ran jaririn yasa mahaifiyar ta shigar da kara ofishin 'yan sanda kuma aka damke faston da mukarrabanta

Mabiya addini musamman a nahiyar Afirka suna daraja malaman addini saboda suna ganinsu a matsayin wadanda ke kusanci da Allah. Sai dai wasu lokutan wasu malaman addinin sukan yi amfani da wannan damar wajen yaudarar mabiyansu.

An kama limamai da suka kasa tayar da matacce bayan sunce za su iya

An kama limamai da suka kasa tayar da matacce bayan sunce za su iya
Source: Twitter

Mun samo cewar 'yan sanda sun kama wata fasto, Viola Nassanga da masu taimaka mata a garin Luweero da ke Uganda bayan wani jariri dan watanni biyar ya rasu a hannunsu.

An ruwaito cewar mahaifiyar yaron, Asineyi Biira, ta fadawa faston cewar jaririnta na fama da rashin lafiya hakan yasa faston ta shawarci Biira ta kawo jaririn domin ayi masa addu'a.

DUBA WANNAN: Gwamnoni 5 da suka fi sauran takwarorinsu a Najeriya

Sai dai bayan faston ta karbi jaririn, ba'a sake jin duriyarsu ba har sai da labari ya fara yaduwa cewar jaririn ya rasu. Hakan yasa mahaifiyar yarinyar ta kai kara wajen 'yan sanda kuma aka kama faston tare da gawar jaririn.

'Yan sandan sun kama Nassanga da masu taimaka mata, Juliet Nakayenga da Edith Nabuule har ma da mai gidan hayar da aka kama daki domin yiwa jaririn addu'a, Lazaro Walakira.

Rahotanni sunce bayan mahaifiyar jaririn ta ji labarin mutuwar, faston ta umurce ta ta kwantar da hankalinta domin za ta dawo wa da jaririn ransa sai dai hakan bai yiwu ba.

Sauran fastocin da ke Cocin Luweero sun nesanta kansu daga Viola Nassanga inda suka yi ikirarin cewar maita ta ke yi ba addinin kirista ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel