Marafa yayi wa Gwamna Yari wankin babban bargo akan zaben fidda gwani a Zamfara

Marafa yayi wa Gwamna Yari wankin babban bargo akan zaben fidda gwani a Zamfara

- Sanata Kabiru Marafa ya caccaki Gwamnan jihar Zamfara akan zaben fidda gwani

- Marafa ya bayyana kira da Gwamna Abdulaziz Yari yayi ga mabiya APC na gudanar da zaben fidda gwani da kansu a matsayin rashin tsari

- Yace abun da Yari ke so shine satar dukiyar jihar amma ba wai ci gaban mutanen jihar ba

Shugaban kwamitin man fetur a majalisar dattawa, Sanata Kabiru Marafa ya bayyana kira da Gwamna Abdulaziz Yari na jihar Zamfara yayiwa mambobin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na gudanar da zaben fidda gwani da kansu a matsayin rashin tsari.

Ya kuma bayyana kiran da gwamnan yayi a matsayin ba bisa doka ba.

Marafa yayi wa Gwamna Yari wankin babban bargo akan zaben fidda gwani a Zamfara

Marafa yayi wa Gwamna Yari wankin babban bargo akan zaben fidda gwani a Zamfara
Source: Getty Images

A yayinda yake jawabi ga manema labarai a Gusau, babban birnin jihar Zamfara Yari ya bukaci dukkanin mabiya jam’iyyar da su gudanar da zaben fidda gwani da kansu domin cimma wa’adin ranar da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta bayar.

KU KARANTA KUMA: Za mu tsige Saraki idan majalisar dokoki ta dawo – Shugaban masu rinjaye a majalisa ya sha alwashi

A wani jawabi da ya saki a ranar Lahadi, 7 ga watan Oktoba, Marafa, daya daga cikin yan takarar gwamna yace kira ga mambobin jam’iyyar da su gudanar da zaben ba tare da masu kula ba daga sakatariyar kasar zai haifar da rashin tsari.

Ya bukaci mabiya jam’iyyar da kada su saurari Gwamnan, cewa Yari na son satar dukiyar jihar ne kawai ba wai son ci gaban mutanen jihar ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel