Mun shirya ma zaben 2019: Oshiomhole ga masu adawa

Mun shirya ma zaben 2019: Oshiomhole ga masu adawa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu kuri’u 14, 842, 072 a lokacin zaben fidda gwani da aka gudanar a fadin jihohi 36 na tarayyar kasar inda hakan ya bashi damar zama dan takarar APC na shugaban kasa a zaben 2019.

A wannan zaben jihohin Kano da Lagas ne suka hada masa kuri’u 5,148,957 yayinda Abia ta samar masa kuri’u mafi karanci guda 043,308 daga mambobin jam’iyyar.

Don haka shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole, yace tunda Shugaba Buhari ya zamo dan takarar jam’iyyar, toh jam’iyyar ta shirya ma zaben 2019.

Mun shirya ma zaben 2019: Oshiomhole ga masu adawa

Mun shirya ma zaben 2019: Oshiomhole ga masu adawa
Source: Depositphotos

Ya fadi hakan ne a jawabin maraba da yayi a wajen babban taron jam’iyyar na kasa da aka gudanar a ranar Asabar.

KU KARANTA KUMA: Tsohon hadimin Abacha ya lashe zaben fidda gwani na shugaban kasa a PPN

Oshiomhole yace shugaban kasar ya yi shugabanci nagari wanda hakan zai zame masa garkuwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel