Da dumi-dumi: Hukumar DSS ta garkame Sanata Kabiru Marafa

Da dumi-dumi: Hukumar DSS ta garkame Sanata Kabiru Marafa

Hankalin jama’a ya tashi a City King Hotel, Gusau a jihar Zamfara inda aka gudanar ganawar masu ruwa da tsakin jam’iyyar APC yayinda fada ya barke tsakanin Sanata Kabiru Marafa da tsohon ministan sadarwa, Alhaji Ikra Aliyu Bilbis.

Wadannan yan siyasa biyu su baiwa hammatan juna iska kan rikicin da yaki ci yaki cinyewa a zaben fidda gwanin gwamnan jihar Zamfara.

Jaridar Leadership ta bada rahoton cewa diraktan DSS na jihar Zamfara ya umurci jami’ansa su tafi da Sanata Marafa amma dogaransa suka ki, daga baya, Marafa ya amince da binus ofishin DSS.

KU KARANTA: Shugabancin kasa: Atiku na mafarki ne kawai – Lauretta Onochie

Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa Sabani kan hanyar da za ai amfani da ita wajen fitar da ‘yan takara a jam’iyyar APC a jihar Zamfara ya kai ga bawa hammata iska tsakanin ‘yan takara.

Rikicin ya afku ne bayan an gaza cimma daidaito a kan tsarin da a ai amfani das hi wajen fitar da ‘yan takarar a jam’iyyar APC.

Tun da fari sai da kwamitin tsara zaben da uwar jam’iyyar APC ta turo ya fitar da tsarin da za a yi amfani da shi don gudanar da zaben, amma sai bangare na ‘yan takarar suka nuna rashin gamsuwa da tsarin, lamarin ya jawo barkewar cece-kuce da musayar yawu da ta kai ga har an bawa hammata iska.

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa damu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel