Tsohon hadimin Abacha ya lashe zaben fidda gwani na shugaban kasa a PPN

Tsohon hadimin Abacha ya lashe zaben fidda gwani na shugaban kasa a PPN

- Hamza Al-Mustapha ya zamo mai nasarar mallakar tikitin shugaban kasa a zaben fidda gwani na jam’iyyar Peoples Party of Nigeria (PPN)

- Tsohon hadimin Abachan ya kayar da sauran yan takara 2 da kuri’u 3,564,262

- Yayi wa ýan Najeriya alkawarin shugabanci mai inganci sannan yayi alkawarin ceto kasar ya mayar da ita kan hanyar ci gaba

Hamza Al-Mustapha, tsohon shugaban tsaron marigayi tsohon shugaban kasa a mulkin soja, Sani Abacha a ranar Lahadi, 7 ga watan Oktoba ya zamo mai nasarar mallakar tikitin shugaban kasa a zaben fidda gwani na jam’iyyar Peoples Party of Nigeria (PPN).

Al-Mustapha ya kayar da sauran yan takara 2 da kuri’u 3,564,262, jaridar The Punch ta ruwaito.

Tsohon hadimin Abacha ya lashe zaben fidda gwani na shugaban kasa a PPN

Tsohon hadimin Abacha ya lashe zaben fidda gwani na shugaban kasa a PPN
Source: UGC

Sauran yan takaran biyu . Imuetinyan Igbinnosa da Cif Isiaka Olorunnimbe, sun samu kuri’u 2,183,856 da 1,400,755.

KU KARANTA KUMA: Za mu tsige Saraki idan majalisar dokoki ta dawo – Shugaban masu rinjaye a majalisa ya sha alwashi

Shugaban kwamitin zaben fidda gwanin kuma shugaban PPN a Ekiti, Dare Adekolu, ya kaddamar da Al-Mustapha a matsayin wanda yayi nasara bayan karban sakamako daga jihohi 36 da babban birnin tarayya.

Al-Mustapha, wanda bai samu halartan taron ba ya samu wakilcin Zakaria Husseini.

Yayi wa ýan Najeriya alkawarin shugabanci mai inganci sannan yayi alkawarin ceto kaasar ya mayar da ita kan hanyar ci gaba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel