2019: Atiku ya fara neman wanda zai tafi da shi a matsayin mataimakinsa

2019: Atiku ya fara neman wanda zai tafi da shi a matsayin mataimakinsa

- Zababen dan takarar shugabancin kasa na PDP, Atiku Abubakar ya fara neman mataimaki da za suyi takara a 2019

- Ana kyautata zaton Atiku zai zabo mataimakinsa ne daga yankin Kudu maso Gabas

- Kungiyar Kabilar Ohanaeze Ndigbo ta tunatar da Atiku cewar ya kamata ya zabi dan kabilar Igbo a matsayin mataimakinsa

A ranar Lahadi da ta gabata ne tsohon mataimkin shugban kasa, Atiku Abubakar ya lashe tikitin takarar shugbancin kasa karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) bayan an gudanar da zaben fidda gwani a Port Harcourt.

Jim kadan bayan sanarwar nasarar Atiku ne mutane suka fara zancen wanda Atiku zai zaba a matsayin mataimakinsa da za suyi takarar zabe a 2019.

2019: Atiku ya fara neman wanda zai tafi da shi a matsayin mataimakinsa

2019: Atiku ya fara neman wanda zai tafi da shi a matsayin mataimakinsa
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Gwamnoni 5 da suka fi sauran takwarorinsu a Najeriya

Binciken da Punch ta gudanar ya nuna cewa akwai yiwuwar Atiku zai zabo mataimakinsa ne daga yankin Kudu maso gabashin Najeriya.

Kazalika, Kungiyar kabilar Igbo Ohanaeze Ndigbo ta fitar da sanarwar tunatar da Atiku da jam'iyyar PDP cewa ya kamata jam'iyyar ta zabo mataimakin shugaban kasa daga yankin Kudu maso Gabas domin yankin su san ana damawa da su.

Atiku ya lashe zaben fidda gwanin ne da kuri'u 1,532 a cikin kuri'u 3,221 wanda hakan ke nuna ya samu kusan 50% na kuri'un jam'iyyar. Mai biye da shi Gwamna Tambuwal na jihar Sokoto ya samu kuri'u 693 yayin da Bukola Saraki da ya zo na 3 ya samu kuri'u 317.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel