Gwamnan Kaduna Malam El-Rufai yayi kaca-kaca da Jam’iyyar PDP

Gwamnan Kaduna Malam El-Rufai yayi kaca-kaca da Jam’iyyar PDP

Kwanaki ne aka yi ta yada cewa Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai yayi kaca-kaca da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Adams Oshimhole. Gwamman ya karyata wannan batu kwanan nan.

Gwamnan Kaduna Malam El-Rufai yayi kaca-kaca da Jam’iyyar PDP

El-Rufai ya musanya cewa sun samu sabani da Shugaban APC a Abuja
Source: UGC

Gwamna Nasir El-Rufai ya nuna cewa rade-radin da ake yi na cewa ya samu matsala da Adams Oshiomhole a dalilin kujeran Sanatan Kaduna ta tsakiya a Jam’iyyar APC karya ce kurum da wasu ke kitsawa saboda ribar siyasa.

Gwamnan na Jam’iyyar APC yayi amfani da shafin sa na Tuwita inda ya karyata wannan magana ya kuma daura laifin yada wannan karya wajen wani da ake zargi yana kusa-da tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan a baya.

KU KARANTA: Ban aiki Gwamnan Kaduna ya casa Sanata Shehu Sani ba - Buhari

Nasir El-Rufai yake cewa tuni Ubangiji ya tsinewa Jam’iyyar adawa ta PDP albarka kuma haka za ta kare yana mai addu’ar Allah ya kara tona mata asiri. Gwamnan ya tsinewa masu yada labaran karya a fadin kasar nan albarka.

Gwamnan dai tsohon ‘Dan Jam’iyyar PDP ne kafin 2014 inda ya rike mukamai da dama a lokacin Gwamnatin Obasanjo daga 1999 zuwa 2007. Daga ciki Gwamnan na yanzu yayi Ministan babban Birnin Tarayya Abuja a 2003.

Kun ji cewa Shugaban kasa Muhammad Buhari ya fito yayi bayani inda ya bayyana cewa bai aiki Gwamnan Jihar Kaduna ko wanin sa ya hukunta Sanata Shehu Sani ko wani ‘Dan APC ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel