2019: Jam’iyyu 39 na shirin dinkewa da Atiku

2019: Jam’iyyu 39 na shirin dinkewa da Atiku

- Gamayyar jam’iyyun siyasa 39 sun kaddamar da shirinsu na daukar Atiku Abubakar a matsayin dan takarar shugaban kasa na hadin gwiwa

- Sunce zasu dinke da shi a matsayin dan takarar hadin gwiwa a zaben saboda suyi waje da shugaban kasa Muhammadu Buhari

- A wata sanarwa da jam’iyyar CUPP ta saki a daren jiya tace shirin dinkewar zai fara a wannan makon

Kasa da sa’o’i shida bayan tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar yayi nasarar zama dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben 2019, wata gamayyar jam’iyyun siyasa 39 sun kaddamar da shirinsu na daukarsa a matsayin dan takarar shugaban kasa na hadin gwiwa.

Jam’iyyun karkashin lemar Coalition of United Political Parties (CUPP), wanda PDP ke jagoranta sunce zasu dinke da shi a matsayin dan takarar hadin gwiwa a zaben saboda suyi waje da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

2019: Jam’iyyu 39 na shirin dinkewa da Atiku

2019: Jam’iyyu 39 na shirin dinkewa da Atiku
Source: UGC

A wata sanarwa da jam’iyyar CUPP ta saki a daren jiya ta hannun kakakinta, Ikenga Ugochinyere tace shirin dinkewar zai fara a wannan makon.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Atiku ya samu kuri'u 1,532 da suka ba shi nasara a kan Tambuwal, da ya zo na biyu da kuri'u 693 da kuma ragowar 'yan takara 10.

KU KARANTA KUMA: Gwamnan Kaduna Malam El-Rufai yayi kaca-kaca da Jam’iyyar PDP

An haska zaben kai tsaye a gidajen talabijin, kuma masu sa ido sun yaba da yadda aka gudanar da zaben ba tare da wata alama ko wani abu na magudi da karya doka ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel