2019: Obasanjo ya saki sabon sako bayan sanar da Atiku a matsayin dan takarar PDP

2019: Obasanjo ya saki sabon sako bayan sanar da Atiku a matsayin dan takarar PDP

A yayin da ake cigaba da tattaunawa da bayyana mabanbantan ra’ayi a kan nasarar da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya samu a zaben fitar dad an takara na jam’iyyar PDP da aka sanar a yau, tsohon shugaban kasa Obasanjo ya bayyana nasa ra’ayin.

A wani sako da tsohon shugaban kasa Obasanjo ya fitar a shafinsa na Tuwita (@chief_obasanjo), Obasanjo ya bayyana cewar, “Allah ya sani bani da wani mugun nufi a kan Atiku, amma a matsayina na mai kishin kasa dole na sanar da ‘yan Najeriya cewar a watan Yuni na shekarar 2006 mun samu wata takarda daga kasar Amurka dauke da jerin sunayen wasu mutane da ya kamata mu bincika, kuma cikinsu har da Atiku.

“Daga shekarar 2006 zuwa yanzum har yanzu Atiku bai kara saka kafarsa cikin kasar Amurka ba, ni kuma ban san dalilinsa na kauracewa kasar Amurka ba.

Dangabtaka tsakanin Atiku da Obasanjo ta dade da lalacewa, kuma duk kokarin ganin an yi sulhu a tsakanin shugabannin biyu ya ci tura.

2019: Obasanjo ya saki sabon sako bayan sanar da Atiku a matsayin dan takarar PDP

Obasanjo da Atiku
Source: Depositphotos

A wani labarin na Legit.ng kun ji cewar sa’o’i kadan bayan an sanar da cewar Atiku ne ya lashe zaben fitar da dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, jam’iyyar APC ta taya shi murna tare da yi masa maraba cikin takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2019.

Atiku, mai shekaru 72, ya samu kuri’u 1,532 da suka ba shi dammar kayar da ragowar ‘yan takara 11 da suka tsaya neman tikitin takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP.

DUBA WANNAN: Abun kunya: 'Yan takarar APC sun bai wa hammata iska a jihar Zamfara (Hoto)

Kakakin kwamitin neman yakin shugaba Buhari, Mista Festus Keyamo, ya yiwa Atiku murnar samun nasara da kuma yi masa marhabun zuwa cikin kamfen din shugaban kasa.

Ya bayyana cewar ‘yan Najeriya yanzu na da zabi tsakanin ‘yan takara biyu: daya mai kima, daya kuma dake fama da matsalar kaurin suna ta fuskar almundahana.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel