Mamba a kwamitin yakin zaben Buhari ya taya Atiku murna, ya yi masa maraba da shigowa takara

Mamba a kwamitin yakin zaben Buhari ya taya Atiku murna, ya yi masa maraba da shigowa takara

Sa’o’i kadan bayan an sanar da cewar Atiku ne ya lashe zaben fitar dad an takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, jam’iyyar APC ta taya shi murna tare da yi masa maraba cikin takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2019.

Atiku, mai shekaru 72, ya samu kuri’u 1,532 da suka ba shi dammar kayar da ragowar ‘yan takara 11 da suka tsaya neman tikitin takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP.

Kakakin kwamitin neman yakin shugaba Buhari, Mista Festus Keyamo, ya yiwa Atiku murnar samun nasara da kuma yi masa marhabun zuwa cikin kamfen din shugaban kasa.

Ya bayyana cewar ‘yan Najeriya yanzu na da zabi tsakanin ‘yan takara biyu: daya mai kima, daya kuma dake fama da matsalar kaurin suna ta fuskar almundahana.

Mamba a kwamitin yakin zaben Buhari ya taya Atiku murna, ya yi masa maraba da shigowa takara

Atiku yayin gabatar da jawabin godiya bayan sanar da sakamako
Source: UGC

A sakon da ya fitar a shafinsa na tuwita, Keyamo, ya ce “muna yiwa Atiku murnar shigowa tarragon kamfen din shugaban kasa na shekarar 2019.

DUBA WANNAN: Abun kunya: ‘Yan takarar APC sin bawa hammata iska a Zamfara, hoto

“Mutanen Najeriya yanzu na da zabi tsakanin nagarta da cin hanci. Dan takara daya na da kima da tarihi mai kyau, daya na fama da zargin almundahana da rashawa.”

Kazalika, shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, ya taya Atiku murna tare da yin alkawarin yin aiki tare domin tabbatar da ya samu nasara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel