Manyan ‘Yan siyasan da ake hangen za su iya zama Mataimakin Atiku Abubakar a PDP

Manyan ‘Yan siyasan da ake hangen za su iya zama Mataimakin Atiku Abubakar a PDP

Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar ne wanda ya lashe zaben fitar da gwani na Jam’iyyar PDP. Yanzu dai ana jira a ji wanene zai zama ‘Dan takarar da zai tafi tare da Atiku domin ya kara da Buhari a zaben 2019.

Manyan ‘Yan siyasan da ake hangen za su iya zama Mataimakin Atiku Abubakar a PDP

An fara harsashen wa Atiku Abubakar zai tsaida a PDP
Source: Depositphotos

1. Peter Obi

Wasu na ganin cewa Atiku zai nemi ya tsaida Peter Obi a matsayin ‘Dan takarar Mataimakin Shugaban kasan sa a 2019. Obi dai tsohon Gwamna ne na Jihar Anambra wanda ya san aiki ya kuma iya Magana game da farin jini.

2. Ben Murray Bruce

Sanata Ben Bruce yana cikin sahun wadanda ake tunani Atiku zai tafi da su a 2019. Sanatan na Bayelsa ta Gabas dai ba zai koma kujerar sa ba don haka ake ganin cewa watakila ya bi Atiku Abubakar wanda tun ba yau ba su ke tare a PDP.

KU KARANTA: Shin ku na ganin Atiku zai yi nasara a 2019 ko kuwa?

3. Oby Ezekwesili

Tsohuwar Ministar ilmin kasar nan Oby Ezekwesili tana cikin mutanen da ake ganin Atiku na iya zama ta masa Mataimakiyar Shugabar kasa. Oby za ta samu karbuwa a wajen manyan ‘Yan Boko da kuma Mata musamman a Kudancin kasar nan.

4. Ngozi Okonjo Iweala

Wata matar da ake kishin-kishin din cewa Atiku zai zama yayi takara da ita a 2019 ita ce Okonjo Iweala wanda tayi Ministar kudi har sau 2 a Najeriya. Iweala dai ta san harkar tattali kuma ita ma tayi aiki da Atiku a lokacin Gwamnatin Obasanjo.

5. Akinwumi Adesina

Na karshe a jerin da ake ganin Atiku na iya zabowa a matsayin ‘Dan takarar Mataimakin Shugaban kasa a PDP shi ne Adesina wanda yanzu shi ne Shugaban bankin nan na cigaban Afrika. Adesina Bayarabe ne da ya rike Ministan noma a Gwamnatin PDP.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel