2019: Jama’a sun tofa albarkacin bakin su bayan nasarar Atiku

2019: Jama’a sun tofa albarkacin bakin su bayan nasarar Atiku

Dazu ne dai labari ya isa Duniya cewa tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar ya lashe zaben fitar da gwani na Jam’iyyar PDP inda zai yi takarar Shugaban kasa da Muhammadu Buhari a zaben 2019.

2019: Jama’a sun tofa albarkacin bakin su bayan nasarar Atiku

Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar da Shugaban PDP
Source: Facebook

Mun kawo kadan daga cikin manyan bayanin da wasu masu bibiyar siyasa a kasar su ke yi. Ga kadan daga ciki:

Ina taya Atiku murnar wannan nasara na samun tikitin PDP domin takarar badi. Na jinjinawa irin wannan namijin kokari da jajircewa na Atiku a fagen siyasa inda ya fara kafa sunan sa tun shekaru 25 da su ka wuce a lokacin Marigayi MKO Abiola.

- Inji Dele Momodu

Wani kuma yace:

Atiku ya nuna Gwamna Wike cewa akwai banbancin wanda ya koyi siyasa wajen Shehu Yaradua da kuma masu yi wa Abokan adawar su barazana a gaban Talabijin Duniya.

- Japheth Omojuwa

KU KARANTA: Wani tsohon Minista ya mutu a wajen da aka zabi Atiku

A 2019 dai za a kara ne tsakanin Muhammadu Buhari mai shekaru 76 da kuma Atiku Abubakar mai shekaru 72 a Duniya. Ko wanene na zaba tsakanin su?

- Ebuka Uchendu

Wani Masoyin Rabiu Musa Kwankwaso kuwa cewa yayi:

Wata guda da su ka wuce na ji Dr. Hakeem Baba-Ahmed yana cewa manyan ‘Yan takaran Shugaban kasa da su ka fi karfi a PDP mutum 3 ne; Aminu Tambuwal, Bukola Saraki da Atiku Abubakar. Yanzu kam na fahimci gaskiya.

- Abubakar Dadiyata

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel