Da duminsa: An sanar da mutuwar tsohon ministan PDP a wurin zaben da Atiku ya lashe

Da duminsa: An sanar da mutuwar tsohon ministan PDP a wurin zaben da Atiku ya lashe

A yayin da ake tsaka da taron gangamin jam'iyyar PDP a Fatakwal bayan sanar da Atiku a matsayin wanda ya lashe zaben dan takarar shugaban kasa, shugaban PDP ya sanar da mutuwar John Odeh.

John Odeh, tsohon ministan yada labarai ya mutu ne a yau, kamar yadda Secondus ya sanar.

Bayan sanar da labarin mutuwar tsohon minista Odeh, Secondus ya bukaci a yi shiru na tsawon minti daya domin nuna juyayin rashin tsohon ministan.

Kafin wannan labarin, Legit.ng ta sanar da ku cewar duk da an sanar da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, a matsayin mutumin da ya yi nasarar lashe tikitin takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, har yanzu taro bai kare ba.

Da duminsa: An sanar da mutuwar tsohon ministan PDP a wurin zaben da Atiku ya lashe

Uche Secondus
Source: Depositphotos

Amma abin mamaki sai ga shi mai masaukin baki, gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya yi wuf ya fice daga filin taron. Wike ya fice ne bayan ya gaisa a gur-guje da Atiku domin yi masa murna. Da ficewar gwamnan magoya bayansa suka dunguma suka bi bayansa.

DUBA WANNAN: Tabbatar da Buhari a matsayin dan takarar APC: Abu 5 da ya fada a jawabinsa

Gwamna Wike na sahun gaba a cikin jiga-jigan 'ya'yan jam'iyyar PDP dake goyon bayan takarar gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel