Muhimman abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da Atiku Abubakar - dan takarar PDP a 2019

Muhimman abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da Atiku Abubakar - dan takarar PDP a 2019

Atiku Abubakar dai dan asalin wani gari ne da ake kira Jada, jihar Adamawa kuma an haife shi ne a ranar 25 ga watan Nuwamba, 1946 kuma shi kadai ne ya rayu a cikin 'ya'yan da mahaifan sa suka haifa a tare.

Sakamakon zaben fitar da gwani na dan takarar shugabancin kasar nan da zai kalubalanci Buhari daga PDP a shekarar, 2019 dai yanzu ya nuna cewa Atiku Abubakar ne ya lashe zaben.

Muhimman abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da Atiku Abubakar - dan takarar PDP a 2019

Muhimman abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da Atiku Abubakar - dan takarar PDP a 2019
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Aisha Buhari tayi kaca-kaca da Oshiomhole

Ga wasu muhimman bayanan da ya kamata ku sani game da dan takarar:

1. Ilimi

Atiku Abubakar ya yi makarantu da dama kama daga Furafare zuwa Sakandare da Difuloma da ma wasu tarin kwasa-kwasai da yayi kafin shigar sa siyasa.

2. Iyalan sa

Atiku Abubakar dai maraya ne domin duka iyayen sa sun rasu kuma yana da mata 4 yanzu da 'ya'ya 27.

3. Dukiya

Atiku Abubakar yana da tarin dukiya domin yana da manyan kamfanoni da dama a ciki da wajen Najeriya.

4. Siyasa

Atiku Abubakar fitaccen dan siyasa ne da ke da dumbin jama'a a kusan dukkan lungu da sako na kasar nan kuma ya fara siyasa ne tun yana da shekaru 34 a duniya.

5. Takarar sa

Atiku Abubakar yayi takarar shugabancin kasar Najeriya a shekarar 2007, da yemi tikitin takarar shugabancin kasar a 2011 da 2015. Yanzu kuma ya samu tikitin takarar PDP a zaben 2019.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel