An fara: Gwamnan PDP da bai ji dadin nasarar Atiku ba ya yi wuf ya fita daga wurin taro

An fara: Gwamnan PDP da bai ji dadin nasarar Atiku ba ya yi wuf ya fita daga wurin taro

Duk da an sanar da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, a matsayin mutumin da ya yi nasarar lashe tikitin takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, har yanzu taro bai kare ba.

Amma abin mamaki sai ga shi mai masaukin baki, gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya yi wuf ya fice daga filin taron.

Wike ya fice ne bayan ya gaisa a gur-guje da Atiku domin yi masa murna. Da ficewar gwamnan magoya bayansa suka dunguma suka bi bayansa.

Gwamna Wike na sahun gaba a cikin jiga-jigan 'ya'yan jam'iyyar PDP dake goyon bayan takarar gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal.

An fara: Gwamnan PDP da bai ji dadin nasarar Atiku ba ya yi wuf ya fita daga wurin taro

Atiku da Wike
Source: Twitter

Ya zuwa lokacin da aka wallafa wannan rahoto babu wanda daga cikin Wike ko Tambuwal ya yi magana a akan sakamakon zaben.

Atiku ya samu kuri'u 1,532 da suka ba shi nasara a kan Tambuwal, da ya zo na biyu da kuri'u 693 da kuma ragowar 'yan takara 10.

DUBA WANNAN: Tabbatar da Buhari a matsayin dan takara: Abu 5 da ya fada a jawabinsa

An haska zaben kai tsaye a gidajen talabijin, kuma masu sa ido sun yaba da yadda aka gudanar da zaben ba tare da wata alama ko wani abu na magudi da karya doka ba.

Cikakken sakamakon zaben PDP:

Kuri'un da suka lalace : 68

Jonah Jang: 19

Datti Ahmed: 05

David Mark: 35

Tanimu Turaki: 65

Sule Lamido: 96

Attahiru Bafarawa: 48

Ibrahim Dankwambo: 111

Ahmed Makarfi: 74

Rabi'u Kwankwaso: 158

Bukola Saraki: 317

Aminu Tambuwal 693

Atiku 1,532 - Zakara

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel