Tabbatar da Buhari a matsayin dan takara: Abu 5 da ya fada a jawabinsa

Tabbatar da Buhari a matsayin dan takara: Abu 5 da ya fada a jawabinsa

A jiya ne wakilai, shugabanni da masu ruwa da tsaki a tafiyar da jam'iyyar APC mai mulki suka tattara a Abuja domin tabbatar da shugaba Buhari a matsayin dan takarar shugaban kasa bayan nasarar da ya samu a zaben fitar da dan takara da aka gudanar a fadin Najeriya.

Da yake sanar da sakamakon zaben, zababben gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, wanda shine shine shugaban kwamitin taron, ya bayyana cewar a kalla daliget 7,000 daga fadin jihohin Najeriya 36 ne suka tabbatar da shugaba Buhari a matsayin dan takarar APC.

Ga wasu abubuwa 5 da Buhari ya fada a jawabinsa

Tabbatar da Buhari a matsayin dan takara: Abu 5 da ya fada a jawabinsa

Tabbatar da Buhari a matsayin dan takara a jiya
Source: Facebook

1. "Jama'a, maza da mata, ina matukar godiya da irin goyon baya da yarda da ni da ku ka nuna."

2. "'Yan uwa na 'yan jam'iyyar APC, ina tsaye a gabanku ne a matsayin dan takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar APC a zaben shekarar 2019."

DUBA WANNAN: Da biyu: An hana manema labarai shiga wurin zaben da Sanata Shehu Sani ya janye

3. "Kun nuna min karamci matuka, kuma hakan ya bani karfin gwuiwa sosai."

4. "Na karbi nauyin da ku ka dora min kuma zamu yi aiki tare domin cigaba da abin alheri da APC ta fara zuwa shekarar 2023 da ma gaba da nan"

5. "Ina son ku sani ba zan taba ba ku kunya ba, zan dauki nauyin da ku ka dora min da matukar muhimmanci."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel