Maganar gaskiya Shugaba Buhari ya cancanci lambar yabo daga gare mu - Kwankwaso

Maganar gaskiya Shugaba Buhari ya cancanci lambar yabo daga gare mu - Kwankwaso

Daya daga cikin masu takarar tikitin zaben shugaban kasar Najeriya a karkashin inuwar jam'iyyar PDP kuma tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya ce a hakikanin gaskiya shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya cancanci lambar yabo daga PDP.

Rabi'u Kwankwaso dai ya bayyana cewa saboda irin rawar da Shugaban kasar ya taka wajen maidowa da jam'iyyar PDP daraja da martabar ta a idanun 'yan Najeriya saboda irin salon mulkin sa, ya kamata jam'iyyar ta bashi kyautar girmamawa.

Maganar gaskiya Shugaba Buhari ya cancanci lambar yabo daga gare mu - Kwankwaso

Maganar gaskiya Shugaba Buhari ya cancanci lambar yabo daga gare mu - Kwankwaso
Source: Twitter

Legit.ng ta samu cewa Kwankwaso yayi wannan kalamin ne a lokacin da yake jawabin takaitacce ga wakilan jam'iyyar masu kada kuri'a kafin fara kada kuri'un su a zaben na jam'iyyar ta PDP da ya gudana a garin Fatakwal, babban birnin jihar Ribas.

Haka zalika, Kwankwaso din ya bayar da tabbacin cewa shi ne zai jagoranci zuwa kai wa shugaban kasar wannan lambar yabo idan dai har jam'iyyar ta shirya.

A wani labarin kuma, Uwar gidan shugaban kasar tarayyar Najeriya, Aisha Buhari ta fito fili ta nuna rashin jin dadin ta game da yadda jam'iyyar su ta APC ta gudanar da zabukan fitar da gwani a dukkan matakai a karkashin jagorancin Adams Oshiomhole.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa a wani lokaci can cikin shekarar 2016 Aisha Buhari din ta fito fili ta soki mijin na ta da kuma jam'iyyar sa inda tace idan harkokin jam'iyyar suka cigaba da tafiya a hakan to fa tabbas ba zata mara mata baya ba a 2019.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel