An fara shirin kirga kuri’un zaben tsaida ‘Dan takaran PDP

An fara shirin kirga kuri’un zaben tsaida ‘Dan takaran PDP

Kawo yanzu dai an kammala zaben fitar da ‘Dan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar PDP inda fiye da ‘Yan takara 10 su ke harin karawa da Shugaban kasa Muhammadu Buhari na APC a zabe mai zuwa na 2019.

An fara shirin kirga kuri’un zaben tsaida ‘Dan takaran PDP

Jama'a wajen zaben fitar da ‘Dan takaran PDP a 2019
Source: Original

‘Ya yan Jam’iyya 3,274 ne su ka kada kuri’ar su wajen fitar da ‘Dan takarar Shugaban kasa a PDP. A Jihar Abia inda PDP ta fi yawan ‘Ya ‘ya, mutane 106 ne su ka zabi ‘Dan takarar da zai rikewa Jam’iyyar tuta a zaben 2019.

Ana dai zaben ne a farfajiyar filin wasan kwallon kafa na Adokie Amasiemeka da ke Garin Fatakwal a Jihar Ribas. Ana sa rai dai za a kirga kuri’un da aka kada domin a san wanene yayi nasara a zaben na fitar da gwani.

KU KARANTA: Kwankwaso ya ba tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan hakuri a taron PDP

The Nation ta rahoto cewa Shugaban gangamin wanda shi ne Gwamnan Delta Ifeanyi Okowa yayi kira ga Jama’a su kara hakuri yayin da ake kintsa kuri’un domin a bayyana ‘Dan takarar da yayi nasara a zaben na fitar da gwani.

Daga cikin ‘Yan takaran na PDP akwai Atiku Abubakar, Rabiu Kwankwaso. Tanimu Turaki, Sule Lamido, Attahiru Bafarawa. Sauran ‘Yan takarar sun hada da Dr. Yusuf Baba-Ahmed, Ahmad Makarfi, da kuma Ibrahim Dankwambo.

Daya daga cikin ‘Yan takarar Ahmed Makarfi dai ya musanta cewa ya janye takara kamar yadda ake yadawa. Kakakin yakin neman zaben tsohon Gwamnan watau Mukhtar Sirajo ya bayyana wannan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel