Jam'iyyar APC ta ce Shehu Sani kurum ta sani a kujeran Sanatan Kaduna

Jam'iyyar APC ta ce Shehu Sani kurum ta sani a kujeran Sanatan Kaduna

Babban Sakataren yada labarai na Jam’iyyar APC Yekini Nabena yayi magana game da kujeran Sanatan Kaduna ta tsakiya inda Shehu Sani ya janye hannun sa daga takara a Jam’iyyar APC a tsakiyar zabe.

APC ta ce Shehu Sani kurum ta sani a kujeran Sanatan Kaduna

APC tace Sanata Shehu Sani kurum ta sani a Jihar Kaduna
Source: Twitter

Jam’iyyar tace Sanata Shehu Sani kurum ta sani a cikin ‘Yan takarar Yankin akasin abin da wanda ya lashe zaben fitar da gwani na kujerar ‘Dan Majalisar ya bayyana. APC tace tana nan a kan bakan ta na ba Shehu Sani tikitin 2019.

Mukaddashin Sakataren yada labarai na APC na kasa Mista Yekini Nebena ya fadawa Jaridar DAILY NIGERIAN a jiya da yamma cewa ba ta ba kowani ‘Dan takara dama ya nemi kujerar Sanata a Yankin tsakiyar Kaduna ba.

KU KARANTA: Buhari ya samu kuri'u 14,842,072 a zaben fidda gwanin APC

Babban Hadimin Gwamnan Kaduna watau Uba Sani ne ya lashe zaben Sanata a APC inda yayi ikirarin cewa APC tayi amai ta lashe inda ta janye matakin da ta dauka na kyale Shehu Sani yayi takara babu hamayya a 2019.

Yekini Nabena yace takardun da ake yadawa da sunan cewa APC ta fitar da su na bogi ne domin bai fito daga hannun Jam’iyya ba. Sanata Shehu Sani dai tuni ya janye hannun sa daga takaran inda aka ce ya samu kuri’a 15 rak.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel