An hana manema labarai shiga wurin zaben da Sanata Shehu Sani ya janye

An hana manema labarai shiga wurin zaben da Sanata Shehu Sani ya janye

Wasu jami'an tsaro sun hana dandazon manema labarai shiga wurin zaben fitar da dan takarar kujerar Sanatan Kaduna ta tsakiya da aka gudanar a filin wasanni na Umaru Musa Yar'adua dake garin Zaria.

'Yan jaridar sun taru tare da kayan aikinsu domin shiga wurin zaben su yi aikinsu na yada labarai, amma sai jami'an tsaro suka hana su shiga.

Duk kokarin manema labaran na shawo kan tawagar jami'an tsaron karkashin jagorancin jami'in 'yan sanda na ofishin Samaru, D. Moses, domin shiga wurin zaben ya ci tura.

Da manema labarai suka tambayi Moses ko baya tsoron karya dokar hakkin 'yan jarida, sai ya kada baki ya ce, "na gwammaci na samu matsala da manema labarai a kan na samu matsala da 'yan siyasa, saboda haka ba zan bari ku shiga ba tun da an ce kar na bari ku shiga "

An hana manema labarai shiga wurin zaben da Sanata Shehu Sani ya janye

Shehu Sani da El-Rufa'i
Source: Depositphotos

Kokarin 'yan jaridar na neman kakakin hukumar 'yan sanda na jihar Kaduna, DSP Yakubu Sabo, ya saka baki ta hanyar tsawatar wa Moses bai yi aiki ba, saboda Moses din ya ki karbar waya domin yin magana da shi.

DUBA WANNAN: 'Yan siyasar Najeriya 10 da suka mallaki dumbin dukiya ta ban mamaki

"Ba zan amsa kiran kakakin hukumar 'yan sanda na jihar Kaduna ba saboda gaba nake da shi a aiki. Ko ya kira ni ba zan amsa ba," a cewar D. Moses.

Sai dai kakakin ya bukaci 'yan jaridar da su kwantar da hankalin su domin yana tuntubar na gaba da shi a kan lamarin, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel