2019: Yan Nigeria mazauna kasashen waje sun jaddada goyon bayansu ga tazarcen Buhari

2019: Yan Nigeria mazauna kasashen waje sun jaddada goyon bayansu ga tazarcen Buhari

- Yan Nigeria mazauna kasashen waje sun jaddada goyon bayansu ga tazarcen shugaban kasa Muhammadu Buhari

- Kungiyar ta ce shirin Buhari na bada rance ga kananan 'yan kasuwa da kuma na ciyar da yara dalibai abinci, na bunkasa rayuwar talaka

- Ta ce a yanzu masu saka hannun jari daga kasashen ketare sun samun kwarin guiwa da kuma jin ra'ayin yin kasuwanci a Nigeria saboda Buhari

Abokan shugaban kasa Muhammadu Buhari da suke karkashin kungiyar magoya bayan Buhari da ke zaune a kasashen ketare (BDSG), sun bayyana Buhari a matsayin dan takarar da yafi kowa cancanta a babban zaben 2019.

A cikin wata sanarwa dauke da sa hannun shugaban kungiyar BDSG, na fadin duniya, Mr. Charles Efe Sylvester, ya ce, "Buhari ne dan takara mafi cancanta da ya mallaki tunani da kuma son ganin ya inganta rayuwar jama'a musamman ma talakawa. Hakika shi shugabane da ke gina al'umma don samun makoma tagari a kasar."

KARANTA WANNAN: Da dumi dumi: Saraki na ganawa da wakilan PDP ana tsaka da babban zaben fidda gwani na jam'iyyar

2019: Yan Nigeria mazauna kasashen waje sun jaddada goyon bayansu ga tazarcen Buhari

2019: Yan Nigeria mazauna kasashen waje sun jaddada goyon bayansu ga tazarcen Buhari
Source: Depositphotos

Sylvester ya ce shirin shugaban kasa Buhari na bada rance ga kananan 'yan kasuwa da kuma shirin ciyar da yara dalibai abinci, na bunkasa rayuwar talaka, yana mai jaddada cewa, "Babban sauyin da aka samu a fannin noma, wanda ya samar da yawan shinkafa, yaki da cin hanci da rashawa, na daga dalilan da ke sa mutane kara kaunar Buhari."

Shugaban kungiyar ya ce kusoshin kafa turakun dai-daita tattalin arkin kasar, bunkasa gine gine na ci gaba da habbaka a gwamnatin Buhari, yayin da ya maido da kwarin guiwar masu saka hannun jari daga kasashen waje, zuwa Nigeria don baje kolinsu.

"A yanzu masu saka hannun jari a gwamnatinsa sun samun kwarin guiwa da kuma jin ra'ayin yin kasuwanci a Nigeria," a cewar Sylvester, yana mai bukatar gaba daya 'yan Nigeria da su hada kai tare da fitowa kwansu da kwarkwatarsu don sake zabar shugaban kasa Buhari a zaben 2019.

Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel