PDP 2019: Abubuwan da Bukola Saraki ya taka wadanda yafi sauran 'yan takara dasu

PDP 2019: Abubuwan da Bukola Saraki ya taka wadanda yafi sauran 'yan takara dasu

- Bukola Saraki ne na uku a yanzu a mulkin Najeriya

- Ya fito daga Arewa daga babban gida

- Yanzu yana sa rai zayyi takarar shugaban kasa a 2019

PDP 2019: Abubuwan da Bukola Saraki ya taka wadanda yafi sauran 'yan takara dasu

PDP 2019: Abubuwan da Bukola Saraki ya taka wadanda yafi sauran 'yan takara dasu
Source: Depositphotos

Siyasar Najeriya dai murda-murda da rikita-rikita ce, yau tana yinka gobe ta qi ka. A yau ana can ana yinta ta qare a birnin fatakwal na jihar Ribas, inda PDP mai adawa zata fitar da wanda zai kara da shugaba Buhari a fabrairun badi.

A cikin 'yan takarar akwai wanda a yanzu shine na uku a gwamnati, tunda yana zaune a kujerar shugaban majalisa, wanda yake dan gidan siyasa ne dama tun usuli.

Duk da yadda gwamnati tayi tayi masa tadiya a 2015 zuwa yau, yaki faduwa, ya kuma ki bada kai bori ya hau, wannan na zuwa ne bayan da ya shugabanci juyin mulki ya hada kai da PDP don kwace majalisa daga hannun APC.

DUBA WANNAN: Pastor yace wani babban lamari zai faru kafin 2019

Ga abubuwan da Saraki ke dasu wanda sauran bassu dasu a takaice:

1. Daga Arewa yake.

2. Musulmi ne.

3. Yana zaman na uku a yanzu a gwamnatance.

4. Ya fito daga babban gida na iyayen siyasa.

5. Yayi gwamna sau biyu.

6. Bayarabe ne.

7. Bafillace ne.

8. Matarsa Kirista ce.

9. Ya fito daga yankin tsakiyar Najeriya, masu son suma su dana mulkin kasar nan.

10. Su Obasanjo, IBB da su Dangote na iya mara masa baya, muddin ya ci zaben tsakar daren nan.

11. Yana da kudin gaske, wanda shii ake bukata kafin a ci zabe a Najeriya.

12. Sanata ne.

13. Saka wasu da kanka...

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa damu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel