Da dumi dumi: Saraki na ganawa da wakilan PDP ana tsaka da babban zaben fidda gwani na jam'iyyar

Da dumi dumi: Saraki na ganawa da wakilan PDP ana tsaka da babban zaben fidda gwani na jam'iyyar

Shugaban majalisar dattijai kuma daya daga cikin 'yan takarar kujerar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, ya gana tare da yin jawabi ga wakilan jam'iyyar ta PDP da suka fito daga jihar Imo da Anambra a ci gaba da zaben fidda gwani na jam'iyyar da ke gudana a Fatakwal.

Haka zalika Saraki ya gana da tsohon gwamnan jihar Anambra, Dr. Peter Obi. Wannan na daya daga cikin yanayin yadda 'yan takarar kujera daban daban, wakilan jam'iyya, gwamnoni da kuma sauran masu ruwa da tsaki dama masoya suka mamaye filin da ake gudanar da wannan babban taro.

KARANTA WANNAN: Taron PDP: Dalilan da zasu sa wakilan jam'iyyar su zabi Tambuwal don ya kara da Buhari

Da dumi dumi: Saraki na ganawa da wakilan PDP ana tsaka da babban zaben fidda gwani na jam'iyyar

Da dumi dumi: Saraki na ganawa da wakilan PDP ana tsaka da babban zaben fidda gwani na jam'iyyar
Source: Twitter

A baya Legit.ng ta ruwaito maku cewa Kakakin kungiyar yakin zaben Tambuwal a matsayin shugaban kasa, Dr Okey Ikechukwu, ya ce Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ne kadai wanda zai iya shugabantar Nigeria irin salon mulkin karni na 21, wajen dawo da martar kasar a idon duniya.

Ya bayyana hakan ne a zantawarsa da manema labarai a ci gaba da babban taron jam'iyyar PDP da ke gudana a garin Fatakwal, jihar Rivers a yau Asabar, 6 ga watan Oktoba, inda wakilan jam'iyyar za su zabi dan takarar shugaban kasar da zai kara da Buhari na jam'iyyar APC.

Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel