Tsaro ya yi tsanani yayin zaben fidda gwanin takarar Kujerar gwamna a jihar Imo

Tsaro ya yi tsanani yayin zaben fidda gwanin takarar Kujerar gwamna a jihar Imo

Da sanadin shafin jaridar The Punch za ku ji cewa a yau Asabar an tsananta tsaro yayin gudanar da zaben fidda gwanin takarar kujerar gwamnatin jihar Imo na jam'iyyar APC da wakilai suka kada kuri'unsu a unguwanni 305 dake fadin jihar.

Kamar yadda rahotanni suka bayyana an tsananta tsaro sakamakon shugabancin jam'iyyar da ta soke zaben na farko da aka gudanar a sanadiyar da dambarwa da ta biyo bayan sakamakon zaben zaben kafin ya bayyana.

Tsaro ya yi tsanani yayin zaben fidda gwanin takarar Kujerar gwamna a jihar Imo

Tsaro ya yi tsanani yayin zaben fidda gwanin takarar Kujerar gwamna a jihar Imo
Source: Depositphotos

Binciken manema labarai ya tabbatar da cewa, an gudanar da zaben cikin lumana a fadin jihar yayin da wakilan jam'iyyar suka kada kuri'un su bisa ga ra'ayoyin su na 'yan takara.

KARANTA KUMA: Cikin Hotuna: Nasarar da hukumar Soji tayi kan 'yan Boko Haram a jihar Borno

Rahotanni sun bayyana cewa, bayan zabe fidda gwani takarar kujerar gwamnatin jihar na jam'iyyar APC, an kuma gudanar da zaben fidda gwanayen takara na kujerun 'yan majalisar wakilai da kuma na dattawa.

Legit.ng ta ruwaito cewa, gwamnan jihar Rochas Okorocha, ya na hankoron tikitin takarar kujerar Sanatan jihar Imo ta Kudu a karkashin jam'iyyar sa ta APC.

Na nan tafe, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika muna mika godiyar mu ta musamman a gare ku yayin da kuke ci gaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel