Tanimu Turaki ya janye wa Bukola Saraki a takarar cikin gida ta PDP - Rahotanni

Tanimu Turaki ya janye wa Bukola Saraki a takarar cikin gida ta PDP - Rahotanni

- Rahotanni da bamu tabbatar ba na cewa Turaki ya janye

- Su 12 ke neman tikitin PDP a 2019

- Ana sa rai za'a karke da Kwankwaso, Atiku da Saraki

Tanimu Turaki ya janye wa Bukola Saraki a takarar cikin gida ta PDP - Rahotanni

Tanimu Turaki ya janye wa Bukola Saraki a takarar cikin gida ta PDP - Rahotanni
Source: Twitter

Rahoto daga jihar Ribas, a birnin Fatakwal da muke kokarin tabbatar da sahihancinsa na cewa Kabiru Turaki ya janye daga takararsa ya mara wa Bukola Saraki baya, a zaben cikin gida za za'a yi a yau asabar zuwa lahadi.

An dai ji labarin cewa dala ce kawai ke kuka a tsakaniin 'yan takarkarun, inda ake sayen deleget kamar dai yadda aka saba a siyasar Najeriya.

DUBA WANNAN: Zamu inganta noma da kiwo a kasar nan - Ministan noma

An fi sa rai Atiku ne zai lashe zaben, sai dai ana ganin kamar Bukola Saraki ne babbar barazana ga hakan, inda shi kuma Kwankwaso, ba'a san kullalliyar da yake hada wa a bayan fage ba.

A gefe daya kuma akwai su Tambawal da ake sa rai gwamnoni ke don dora wa.

Karin bayani: Kabiru Turaki a yanzunnan ya fito ya karyata wannan bayanai, yace yana nan daram a takararsa.

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa damu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel