Fitar da dan takarar gwamna a APC: An fara tattara sakamakon zabe a Adamawa, duba

Fitar da dan takarar gwamna a APC: An fara tattara sakamakon zabe a Adamawa, duba

Duk da biyu daga cikin 'yan takarar kujerar gwamnan Adamawa na gudanar da zanga-zanga, an fara tattara sakamakon zaben fitar da dan takarar gwamnan jihar a karkashin jam'iyyar APC.

'Yan takarar biyu - Nuhu Ribadu da Dakta Mahmood Halilu, sun bayyana rashin gamsuwa da zaben da aka fara tun jiya Juma'a.

A cewar Halilu, kayan zabe basu iso da wuri ba, kuma bayan isowar su gwamnati ta yi awon gaba da su.

Fitar da dan takarar gwamna a APC: An fara tattara sakamakon zabe a Adamawa, duba

Gwama Umar Jibrilla Bindo na jihar Adamawa
Source: Depositphotos

A nasa bangaren, Nuhu Ribadu, ya bayyana cewar ba a tantance masu kada kuri'a ba kamar yadda dokar jam'iyya ya tanada ba.

Kazalika ya nemi uwar jam'iyyar APC da ta rushe zaben.

Akwai karin bayani...

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel