Sanata Marafa ya nemi ayi wa masu kokarin murde zaben APC duka a Zamfara

Sanata Marafa ya nemi ayi wa masu kokarin murde zaben APC duka a Zamfara

Mun samu labari cewa Jam’iyyar APC mai mulki ta samu kan ta cikin rikicin cikin gida a Jihar Zamfara a dalilin zaben fitar da ‘Dan takaran Gwamnan Jihar a karkashin APC a zabe mai zuwa 2019.

Sanata Marafa ya nemi ayi wa masu kokarin murde zaben APC duka a Zamfara

Marafa ya nemi Magoya bayan su su zane masu tada rikici
Source: Twitter

Kamar yadda labari ya zo mana, rikicin da ake bugawa a Jam’iyyar APC a Jihar Zamfara yayi mugun kamari inda har ta kai Uwar Jam’iyya ta rusa shugabancin APC na Jihar a lokacin da ake daf da shirin tsaida ‘Dan takarar Gwamna.

Sanata Kabiru Marafa wanda yana cikin masu neman Gwamna a Zamfara a wani bidiyo da ya shigo hannun mu ya umarci magoya bayan sa su yi wa duk wanda su kayi kokarin kawo hatsaniya wajen zaben fitar da gwani na APC.

Kabiru Marafa yayi wannan kira ne lokacin da ya fita yawon kamfe kwanaki inda ya nemi Mutanen sa su takawa duk masu neman tada rikici a wajen zaben APC burki. Sanatan yace a lakadawa duk wanda ya zo wajen akwatin zabe duka.

KU KARANTA: ‘Yan takara sun ki amincewa da zaben fitar da gwani a APC

Marafa wanda yake wakiltar Zamfara ta tsakiya a Majalisar Dattawa ya bayyana cewa a shirye yake Jami’an tsaro su damke sa a sakamakon yi wa masu neman yin magudi a zaben APC na Jihar Zamfara duka da Masoyan na sa su ka yi.

Ana dai sa rai Jam’iyyar APC za tayi maza ta fitar da ‘Dan takarar Gwamna a Jihar inda Sanata Marafa ya gargadi Jam’iyyar cewa idan tayi sake, za a tashi APC ba ta da ‘Dan takarar Gwamna a Zamfara saboda rikicin da ake tayi a Jihar.

Kwanakin kun samu labari cewa rikici ya barke a Gabashin Jihar Neja bayan zaben fitar da gwani na Jam’iyyar APC mai mulki inda Sanatan da ke wakiltar Yankin ya sha kasa a zaben da aka soma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel