Zaben ‘Dan takarar PDP: Fastocin Atiku da Tambuwal sun bi gari a cikin Fatakwal

Zaben ‘Dan takarar PDP: Fastocin Atiku da Tambuwal sun bi gari a cikin Fatakwal

Labarin da mu ke samu tun a jiya shi ne babu hotunan Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki sosai a wajen filin taron Jam’iyyar PDP inda za a tsaida ‘Dan takaran da zai rikewa Jam’iyyar tuta a 2019.

Zaben ‘Dan takarar PDP: Fastocin Atiku da Tambuwal sun bi gari a cikin Fatakwal

Babu fastocin Saraki sosai a filin taron PDP a Ribas
Source: Original

Jaridar Sahara Reporters ta bayyana cewa an rasa fastocin Bukola Saraki a kofar shiga farfajiyar da za ayi zaben tsaida ‘Dan takarar Shugaban kasa na PDP. Akwai dai fastocin sauran ‘Yan takaran irin su Atiku Abubakar a filin babban taron.

Majiyar ta bayyana cewa a jiya da rana babu hotunan Saraki a wajen zaben kamar yadda hotunan sauran masu neman kujerar Shugaban kasar su ka cika ko ina. Za a yi zaben ne a babban filin wasan kwallon kafa da ke Garin Fatakwal.

Akwai dai manyan fastocin tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar kusan 6 da zarar mutum ya shiga farfajiyar zaben. Haka kuma ana hangen manyan fastocin Aminu Waziri Tambuwal a ko ina a cikin Jihar na Ribas.

KU KARANTA: APC na shirin tsaida ‘Dan uwan Buhari takara da karfi da yaji a Daura

Za dai ayi zaben na PDP ne a filin wasa na Adokiye Amasemeka da ke Garin Fatakwal inda’Yan takara fiye da 10 su ke harin kujerar. Daga cikin akwai Rabiu Musa Kwankwaso, Tanimu Turaki, Sule Lamido, da kuma Attahiru Bafarawa.

Sauran ‘Yan takarar sun hada da Dr. Yusuf Baba-Ahmed, Ahmad Makarfi, da Ibrahim Dankwambo. A jiya dai akwai dinbin jama’a dauke da kayan PDP wadanda wasun su ke tare da tsohon Gwamnan Jihar Sokoto Attahiru Bafarawa.

Kun ji cewa zaben tsaida ‘Yan takarar APC ya bar baya da kura a wasu Jihohi inda wasu ‘Yan takara sun rubutawa Shugaban Jam’iyyar APC Kwamared Adams Oshimhole wasika a sake zabe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel