Hankula sun tashi yayin da wani dutse ya rika yin aman wuta a garin Abuja

Hankula sun tashi yayin da wani dutse ya rika yin aman wuta a garin Abuja

- An ga dutse na aman wuta a garin Abuja

- Hankula sun tashi da ganin hakan

- Tawagar gwamnatin tarayya ta ziyarci wurin

Wasu rahotannin da muke samu daga majiyoyin mu sun tabbatar mana da cewa al'ummar mazauna unguwar Mpape dake a garin Abuja, babban birnin tarayya sun kidima bayan da suka ga wani dutsen da ke kusa da su yana aman wuta tare da fitar da hayaki.

Hankula sun tashi yayin da wani dutse ya rika yin aman wuta a garin Abuja

Hankula sun tashi yayin da wani dutse ya rika yin aman wuta a garin Abuja
Source: UGC

Majiyar mu ta Daily Trust har ila yau ta bamu labarin cewa tuni ma har wata kwakkwarar tawaga daga gwamnati da ta hada da ministan birnin Abuja, na ma'adanai da kuma jami'an hukumomin da lamarin ya shafa suka ziyarci wurin domin gane wa idon su.

Legit.ng ta samu cewa sai dai bayan ziyarar ta jami'an gwamnati, sun bayyana cewa al'umma su cigaba da harkokin su na yau da kullum kamar yadda suka saba kafin cikakken rahoto game da lamarin ya fita zuwa 'yan satittikan dake tafe.

Hankulan 'yan garin Abujar dai daman a saman akaifa yake biyo bayan wata girgizar kasa da ta auku a wata unguwa a garin cikin watan da ya gabata.

A wani labarin kuma, Babban ministan harkokin cikin gida kuma mamba a majalisar zartarwar shugaba Buhari, Laftanal Janar Abdulrahman Dambazau ya umurci jami'an tsaron kasar nan da su lalubo hanyoyin da suka dace domin kawo karshen rikicin jihar Filato.

Dambazau, wanda ya nuna jimamin sa da da rashin jin dadi game da yadda rikicin na jihar kan lakume rayuka da dukiyoyi a duk lokacin da ya auku, ya ce dole ne a kawo karshen sa cikin gaugawa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel