Da dumin sa: Wani Gwamna a Arewa ya kira muhimmin taro, yana so fice daga APC

Da dumin sa: Wani Gwamna a Arewa ya kira muhimmin taro, yana so fice daga APC

- Gwamnan Zamfara ya soma shire-shiren ficewa daga jam'iyyar APC

- Ya kira wani taron gaggawa na mukarraban sa

- Jam'iyyar APC a jihar na cikin cakwakiya sosai

Wani labari da ya riske mu ba da dadewa ba na nuni ne da cewa gwamnan jihar Zamfara dake a shiyyar Arewa maso yammacin kasar nan, Abdulaziz Yari ya kira wani taron gaggawa na masu ruwa da tsaki a jihar inda suke tattauna makomar su a siyasance a jihar.

Da dumin sa: Wani Gwamna a Arewa ya kira muhimmin taro, yana so fice daga APC

Da dumin sa: Wani Gwamna a Arewa ya kira muhimmin taro, yana so fice daga APC
Source: Facebook

KU KARANTA: Zaben fitar da gwani: Atiku ya lashe zaben gwani da akayi

Gwamnan na jihar Zamfara da kuma ke zaman shugaban kungiyar gwamnoni ta Najeriya ya kira taron ne na masu rike da mukaman siyasa a jihar da ke goyon bayan sa kuma kamar yadda muka samu hakan bai rasa nasaba da tirka-tirkar da siyasar jihar ke yi.

Legit.ng ta samu daga majiya mai tushe cewa taron da aka gudanar ba'a bari kowa ya shiga da wayar hannun sa ba domin gudun kada abun da suka tattauna ya bulla a waje.

Jam'iyyar APC a jihar ta Zamfara dai na cikin wata cakwakiya biyo bayan rikice-rikicen da ke faruwa dangane da zabukan fitar da gwani na gwamnan jihar.

A wani labarin kuma, Labarin da ke zuwa mana yanzu ba da dadewa ba na nuni ne da cewa tuni masu ruwa da tsaki da ma jiga-jigan jam'iyyar PDP a mataki na kasa suka kammala kulle-kullen baiwa gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal tikitin takarar shugaban kasar su a yau.

Kamar yadda muka samu dai, gwamnan na Sokoto yanzu haka yana da goyon bayan gwamnonin jam'iyya da kuma wasu manya masu fada aji a cikin jam'iyyar ta PDP.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel