Zaben PDP: Kulle-kulle sun yi nisa na kakaba wani gwamna a matsayin dan takarar shugaban kasa

Zaben PDP: Kulle-kulle sun yi nisa na kakaba wani gwamna a matsayin dan takarar shugaban kasa

- Kulle-kulle sun yi nisa na kakaba wani gwamna a matsayin dan takarar shugaban kasa na PDP

- Ana sa ran Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya samu tikitin

- Yanzu haka garin Fatakwal ya dauki harami domin zaben

Labarin da ke zuwa mana yanzu ba da dadewa ba na nuni ne da cewa tuni masu ruwa da tsaki da ma jiga-jigan jam'iyyar PDP a mataki na kasa suka kammala kulle-kullen baiwa gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal tikitin takarar shugaban kasar su a yau.

Zaben PDP: Kulle-kulle sun yi nisa na kakaba wani gwamna a matsayin dan takarar shugaban kasa

Zaben PDP: Kulle-kulle sun yi nisa na kakaba wani gwamna a matsayin dan takarar shugaban kasa
Source: Depositphotos

Kamar yadda muka samu dai, gwamnan na Sokoto yanzu haka yana da goyon bayan gwamnonin jam'iyya da kuma wasu manya masu fada aji a cikin jam'iyyar ta PDP.

Legit.ng ta samu cewa yanzu haka dai garin Fatakwal inda za'a yi zaben na fitar da gwani ya cika makil da jama'a daga sassan kasar nan baki daya domin yin zaben.

Haka zalika mun samu cewa gwamnan jihar ta Ribas, Mista Nyeson Wike yana goyon bayan Tambuwal din kuma shine ma yake jagorantar ganin lallai ya samu nasarar zaben na yau.

A wani labarin kuma, Wani labari da ya riske mu ba da dadewa ba na nuni ne da cewa gwamnan jihar Zamfara dake a shiyyar Arewa maso yammacin kasar nan, Abdulaziz Yari ya kira wani taron gaggawa na masu ruwa da tsaki a jihar inda suke tattauna makomar su a siyasance a jihar.

Gwamnan na jihar Zamfara da kuma ke zaman shugaban kungiyar gwamnoni ta Najeriya ya kira taron ne na masu rike da mukaman siyasa a jihar da ke goyon bayan sa kuma kamar yadda muka samu hakan bai rasa nasaba da tirka-tirkar da siyasar jihar ke yi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel