Duk duniya babu shugaban kasar da bai san abun da yake yi ba kamar na Najeriya - Kukah

Duk duniya babu shugaban kasar da bai san abun da yake yi ba kamar na Najeriya - Kukah

- Shugaban kasar Najeriya bai san abun da yake yi ba inji wani babban malamin addinin Kirista

- Bishop Matthew Hassan Kukah ne ya ce hakan

- Yace dole ne a zo yai gyaran tsarin mulki

Daya daga cikin shehunnan malaman addinin kiristanci a Najeriya kuma shugaban majami'un darikar 'yan Katolika shiyyar jihar Sokoto, Dakta Mattew Hassan Kukah ya bayyana cewa a duk duniya shi bai taba ganin shugaban kasar da bai san aikin sa ba irin na Najeriya.

Duk duniya babu shugaban kasar da bai san abun da yake yi ba kamar na Najeriya - Kukah

Duk duniya babu shugaban kasar da bai san abun da yake yi ba kamar na Najeriya - Kukah
Source: Twitter

KU KARANTA: Akwai yiwuwar APC ta shiga zabe a Zamfara ba gwamna

Dakta Kuka, wanda yayi wannan ikirarin a ranar Juma'ar da ta gabata, ya kuma bayyana cewa su shugabannin kasa a Najeriya sukan murde doka ne suyi yadda suke so da ita idan dai har suka ga damar yin hakan.

Legit.ng ta samu cewa Dakta Matthew Kukah wanda ya gabatar da makala a wajen wani taron lalubo hanyoyin raya kasa a garin Akure, jihar Ondo, ya kuma bayyana cewa lamarin na shugabannin kasar Najeriya yana bashi mamaki matuka.

Daga karshe kuma sai ya shawarci cewa ya kamata a zo ayi gyara a kundin tsarin mulkin kasa domin a rage irin ikon da aka ba shugaban kasa wanda a cewar sa ya wuce misali.

A wani labarin kuma, A shekarar 2015, jim kadan bayan da aka sanar cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya lashe zaben da aka gudanar, wani abun da ya dauki hankalin al'umma shine tattakin da wani matashi yayi daga jihar Legas zuwa Abuja.

Matashin mai suna Suleiman Hashim, a lokacin ya ce yana yin tattakin ne domin taya shugaba Buhari murnan lashe zabe da kuma yiwa 'yan Najeriya murna su ma.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel