Matakin da Buhari ya ce in dauke game da Shehu Sani - El-Rufai

Matakin da Buhari ya ce in dauke game da Shehu Sani - El-Rufai

- Gwamna El-Rufai na jihar Kaduna ya ce Shugaba Buhari ya bashi umurnin yiwa Sanata Shehu Sani kiranye

- An bayar da umurnin yin kiranyen ne saboda irin yankan baya da zagon kasa da Shehu Sani ke yiwa APC

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya ce shugaba Muhammadu Buhari ya bashi umurnin fara yiwa Sanata Shehu Sani kiranye saboda yankan baya da rashin da'a da ya rika yiwa jam'iyyar APC kamar a cewar The Cable.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a wata wasika da ya aike wa shugaban kasa a ranar 2 ga watan Oktoban 2018.

A cikin wasikar, gwamna El-Rufai ya lissafo wasu laifuka da Sanata Shehu Sani ya aikata ga jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da kuma shugaba Muhammadu Buhari.

Buhari ya ce in hora Shehu Sani saboda zagon kasa da ya ke yiwa jam'iyya - El-Rufai

Buhari ya ce in hora Shehu Sani saboda zagon kasa da ya ke yiwa jam'iyya - El-Rufai
Source: Facebook

Har ila yau, gwamnan ya ce yankan bayan da Sanata Shehu Sani ya rika yiwa jihar Kaduna a majalisar dattawa ne ya sanja majalisar ta ki amincewa jihar ta karbi bashin $350m daga bankin duniya.

DUBA WANNAN: An hana ni takara a PDP don na ki amince ayi lalata da ni - Fati Gombe

Wannan na zuwa ne bayan shugaban APC, Adams Oshiomhole ya yiwa Shehu Sani alkawarin tikitin takara ba tare da hamaya ba wanda hakan bai yiwa gwamna El-Rufai da sauran magoya bayansa dadi ba duba da cewa yana son hadiminsa, Uba Sani ya maye gurbin Shehu Sani a majalisa.

Daga baya dai Sanata Shehu Sani ya sanar da cewa ya janye daga takarar wanda hakan ke nuna cewa Uba Sani ne zai samu tikitin takarar na jam'iyyar.

A halin yanzu dai babu tabbas cewa Sanata Shehu Sani da gwamna El-Rufai za su dinke waje guda su cigaba da aiki duba da irin adawar da ke tsakaninsu na tsawon shekaru wadda hakan ya raba kawunan jam'iyyar a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel