Bayyanar Hotunan wasu Maza biyu da suka auri junan su ya janyo cecekuce a Zaurukan sada zumunta

Bayyanar Hotunan wasu Maza biyu da suka auri junan su ya janyo cecekuce a Zaurukan sada zumunta

Bayyanar Hotunan wasu Maza biyu, Riccardo da kuma James Burrell-Hinds, da suka auri junan su ta janyo cecekuce a Zaurukan sada zumunta a yayin da yanayin shagalin bikin ya dauki wani sabon salo da idanu ba su taba kai wa gare shi ba.

Wannan sabon salo musamman yanayin shiga ta amare ko kuma a ce angwayen biyu ta dauki hankulan mutane a yayin bikin da aka gudanar a birnin Paris na kasar Faransa.

KARANTA KUMA: Kotu ta yankewa wani Jami'in 'Dan sanda hukuncin Kisa ta hanyar rataya a jihar Bayelsa

Rahotanni sun bayyana cewa, ma'auratan biyu wanda ke kan sana'a daya ta aiki a wata Mashaya ta sayar da Barasa dake birnin Florida na kasar Amurka, sun kulla yarjejeniyar su ta auren juna a ranar Talata 25 ga watan Satumban da ya gabata.

Ricardo da James sun dauki hotunansu masu daukar hankali a gaban shahararriyar hasumiyar Eiffel, babbar gadar garin Seine da kuma matattakalar bene ta gidan ma'adanan tarihi na Petit Palais.

Na nan tafe, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika muna mika godiyar mu ta musamman a gare ku yayin da kuke ci gaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel