Kotu ta yankewa wani Jami'in 'Dan sanda hukuncin Kisa ta hanyar rataya a jihar Bayelsa

Kotu ta yankewa wani Jami'in 'Dan sanda hukuncin Kisa ta hanyar rataya a jihar Bayelsa

Da sanadin shafin jaridar The Punch mun samu rahoton cewa, wata babbar kotun jiha dake zamanta a birnin Yenagoa na jihar Bayelsa, ta zartar da hukuncin kisa ta hanyar rataya kan wani karamin ma'aikacin dan sanda, Kofura Vincent Koluamawei.

Kotun ta zartar da wannan hukunci kan jam'in dan sandan bisa laifin da ya aikata na kisan wani saurayi ba tare da hakki ba, Innocent Kokorifa mai shekaru 17 a duniya.

Marigayi Innocent yayi kacibus da ajali a ranar 18 ga watan Agustan 2016 yayin da Kofura Vincent ya sheke shi da harsashi na bindiga da Hausawa kan ce idan kaji sautin fitarsa to ga wanin ka ne.

Saurayin wanda daya daga 'ya'ya biyar na wani ma'aikacin hukumar FRSC, Mista Daniel Kokorifa, ya yi gamo da ajali a kan babbar hanyar Barikin Sojin Sama dake birnin Yenagoa a jihar Bayelsa.

Karar kwana da ba ta wuce rana ta sanya jami'in dan sandan cikin gudanar da aikin sa na sintiri ya harbe Marigayi Innocent yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa aiken mahaifiyarsa, Pere Kokorifa.

Kotu ta yankewa wani Jami'in 'Dan sanda hukuncin Kisa ta hanyar rataya a jihar Bayelsa

Kotu ta yankewa wani Jami'in 'Dan sanda hukuncin Kisa ta hanyar rataya a jihar Bayelsa
Source: UGC

Cikin musanta wannan zargi a gaban kotu, hukumar 'yan sandan jihar ta bayyana cewa marigayi Innocent na daya daga cikin mambobin wata kungiyar 'yan fashi da makami da aka harbe yayin musayar wuta da ma'aikata.

Rahotanni sun bayyana cewa, kisan wannan matashi ya janyo boren matasa da kuma kungiyoyi masu kare hakkin dan Adam da suka gudanar da zanga-zanga ta bayyana rashin amincewa.

KARANTA KUMA: Sanata Yarima ya yiwa manema Labarai ta Kurame bayan ganawarsa da Shugaba Buhari

A yayin zartar da hukunci a jiya Juma'a, Alkali Eradiri ya bayyana cewa, bincike ya tabbatar da ba bu wata hujja ko ta sisin kobo daga bangaren hukumar 'yan sandan da a sanadiyar hakan ya zartar da hukuncin kisa ta hanyar rataya ga ma'aikacin ta.

Ya kara da cewa, ba bu wani hukunci da yayi daidai da laifin da ma'aikacin dan sanda ya aikata face hukuncin kisa, inda a halin yanzu kotun ta zartar da wannan hukunci ta hanyar rataya sai dai illa iyaka Mai Kowa mai Komai ya jikan sa.

Nan nan tafe, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika muna mika godiyar mu ta musamman a gare ku yayin da kuke ci gaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel