An dage lokacin fara babban taro na APC a Abuja

An dage lokacin fara babban taro na APC a Abuja

Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) sanar da cewar za'a fara gudanar da taron gangami da fidda gwaninta na kasa ne misalin karfe 6 na yammacin yau Asabar a maimakon 12 na rana da aka sanar a baya.

Sanarwan canjin ta fito ne daga bakin Ciyaman din kwamitin shirye-shirye na taron, Gwamna Abiola Ajimobi na jihar Oyo.

"An matsar da lokacin fara taron ne zuwa yamma saboda a bawa wakilan wasu jihohi da suka kammala zaben fidda gwani a jihohinsu damar zuwa Abuja domin su hallarci taron," inji Ajimobi.

An dage lokacin fara babban taro na APC a Abuja

An dage lokacin fara babban taro na APC a Abuja
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: An hana ni takara a PDP don na ki amince ayi lalata da ni - Fati Gombe

Sanarwan ta kara da cewa za'a tantance dukkan wakilan da za su shigo Abuja a yau a filin matsa jiki na kasa da ke Abuja yayin da wadanda ke Abuja kuma za'a tantance su a tsohuwar filin pareti da ke Area 10 a Abuja.

Ajimobi ya bawa wakilan hakuri bisa canjin inda ya shawarce su da bin hanyoyin da babu cinkoson motocci domin su iso a kan lokaci.

Legit.ng ta tattaro cewa shugaba Muhammadu Buhari ne kawai dan takarar da za'a zaba a wajen taron saboda har yanzu bashi da wani abokin hammaya a jam'iyyar.

Ana sa ran wakila 7,000 ne za su hallarci taron daga jihohi 36 na Najeriya da babban birnin tarayya, Abuja.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel