Sanata Yarima ya yiwa manema Labarai ta Kurame bayan ganawarsa da Shugaba Buhari

Sanata Yarima ya yiwa manema Labarai ta Kurame bayan ganawarsa da Shugaba Buhari

A jiya Juma'a Sanata Ahmed Sani Yarima mai wakilcin mazabar jihar Zamfara ta Yamma a majalisar dattawa, ya yi ganawar sirri tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar sa ta Villa dake babban birnin kasar nan na tarayya.

Sai dai kamar yadda shafin jaridar The Nation ya ruwaito, Sanata wanda ke rike da wannan kujera ta majalisar tarayya karo na uku ya yiwa manema labarai ta Kurame yayin da suke nemi tatsar rahoto a tattare da shi dangane abinda suka tattauna da shugaba Buhari a bayan Labule.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya fahimci cewa, Sanatan ya zayyanawa shugaba Buhari batutuwan da suka shafi harkokin tsaro da kuma siyasa a Mahaifarsa ta Zamfara.

Rahotanni sun bayyana cewa, kafin wannan ganawa ta Yarima da shugaba Buhari, makamanciyar ta ta gudana tsakanin shugaban kasar tare Sanatan jihar Zamfara ta Tsakiya, Sanata Kabiru Marafa.

Sanata Yarima ya yiwa manema Labarai ta Kurame bayan ganawarsa da Shugaba Buhari

Sanata Yarima ya yiwa manema Labarai ta Kurame bayan ganawarsa da Shugaba Buhari
Source: UGC

Marafa yayin ganawarsa da manema labarai na fadar shugaban kasa ya bayyana cewa, ganawarsa da shugaba Buhari ta gudana ne kan soke zaben fidda gwanin takarar na kujerar gwamnatin jihar da kuma yadda al'ummar jihar a halin yanzu suka juya baya ga gwamnan jihar, Abdul'aziz Yari.

KARANTA KUMA: Zaben Fidda Gwani: Gwamna Yari zai kalubalanci shugaban jam'iyyar APC na kasa a jihar Zamfara

Legit.ng ta ruwaito cewa, a ranar Juma'ar da ta gabata shugabancin jam'iyyar APC na kasa ya watsar da shugabannin jam'iyyar reshen jihar tare da kayyade ranakun 6 da kuma 7 ga watan Oktoba domin gudanar da zaben fidda gwanayen takarar kujerar gwamna, majalisar wakilai da kuma ta dattawa na jihar.

Kazalika tsohon sakataren gwamnatin tarayya Mista Anyim Pius Anyim, ya yiwa manema labarai ta kurame a jiya Juma'a bayan ganawarsa da shugaba Buhari da ta gudana a bayan Labule.

Nan nan tafe, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika muna mika godiyar mu ta musamman a gare ku yayin da kuke ci gaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel