Rundunar 'yan sanda ta cafke 'yan bangar siyasa 100 dauke da muggan makamai a Kebbi

Rundunar 'yan sanda ta cafke 'yan bangar siyasa 100 dauke da muggan makamai a Kebbi

Rundunar 'yan sanda ta jihar Kebbi ta cafke sama da yan bangar siyasa 100 bisa laifin kamasu dauke da muggan makamai a lokutan yakin zabe da dama na jihar.

Kwamishinan yan sanda na jihar, Mr. Kabiru wanda ya tabbatar da cafke yan bangar siyasar ga manema labarai a shelkwatar rundunar da ke Birnin Kebbi ya ce rundunar ba zata tsaya a nan ba, zata tabbata ta bi diddigi har ga iyayen gidansu.

KARANTA WANNAN: PDP na zargin APC da yunkurin dakatar da ita daga gudanar da babban taronta na kasa

Rundunar 'yan sanda ta cafke 'yan bangar siyasa 100 dauke da muggan makamai a Kebbi

Rundunar 'yan sanda ta cafke 'yan bangar siyasa 100 dauke da muggan makamai a Kebbi
Source: Depositphotos

Haka zalika, Legit.ng ta ruwaito maku cewa Hukumar hana fasa kwabri ta kasa (Kwastam), sashen 'Zone A' na gwamnatin tarayya, a ranar Alhamis, hukumar ta ce ta samu nasarar cafke kayayyaki daban daban wadanda ba su da takardar DPV da suka kai darajar Naira biliyan biyu.

Daga cikin kayayyakin da aka kama akwai motoci guda 22 wadanda keda garkuwa daga harsashen bindiga, da kudinsu ya kai N1.179bn.

CIKAKKEN LABARIN: Cikin wata 1: Hukumar kwastam ta cafke motoci 22 da kudinsu ya kai N2bn

Hukumar ta ce a sa'ilin da aka cafke wasu motocim a Ogere da Ijebu Ode, an kuma gano wasu motocin da dama a wani gida dake kan tsibirin Victoria, jihar Legas.

A cewar hukumar, sun samu nasarar cafke kayayyakin ne daga 4 ga watan Satumba zuwa 3 ga watan Oktoba.

Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel