Abubuwa 6 da Fayose ya daina yi tun bayan kayar da PDP zaben Ekiti

Abubuwa 6 da Fayose ya daina yi tun bayan kayar da PDP zaben Ekiti

Gawamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ba bakon suna bane a cikin siyasar zamani, musamman yadda ya yi suna wajen sukar shugaba Buhari da APC da kuma nuna wasu halaye dake jawo cece-kuce da tofa albarkacin baki.

A ranar Asabar, 14 ga watan Yuli, 2018 ne aka gudanar da zaben gwamnan Ekiti da Kayode Fayemi, dan takarar APC kuma ministan albarkatun kasa a gwamnatin Buhari ya lashe.

A yayin da zaben ke karatowa ne Fayose ya bayyana cewar PDP ce zata cigaba da mulkin jihar Ekiti saboda shine ke da mutane kuma kullum yake tare da su.

Abubuwa 6 da Fayose ya daina yi tun bayan kayar da PDP zaben Ekiti

Ayo Fayose
Source: UGC

Sai dai tun kafin ya mika mulki ga Fayemi, jama'a sun fara bayyana cewar tun da aka kayar da PDP ya daina aikata wasu abubuwa da yake yi domin samun farinjinin jama'a.

Ga wasu abubuwa 6 da aka gano yanzu Fayose ya daina aikata su.

1. Cin abinci a gefen hanya

2. Suyar garin kwaki tare da mata a kasuwanni

DUBA WANNAN: Mun tura Kwankwaso PDP ne domin ya yi mana wani aiki - Jigo a APC

3. Rabawa jama'a kofin shinkafa a kan titi

4. Yanka cin-cin din murnar zagayowar ranar haihuwarsa

5. Sayen nama tare da ci a gefen titi

6. Zuwa ya kai gyaran takalminsa ciki kasuwa

Wasu daga cikin jama'a na tambaya ko me yasa ya daina wadannan halaye yanzu?

Tuni dai hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC) ta bayyana niyyarta ta binciken Fayose a kan zarge-zargin almundahana da babakere.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel