Yadda wani mutum a Katsina ya kashe diyar makwabcinsa bayan ya yi mata fyade

Yadda wani mutum a Katsina ya kashe diyar makwabcinsa bayan ya yi mata fyade

- An gurfanar da wani mutum da ake zargin ya yiwa diyar makwabcinsa fyade a gaban kotu

- An ruwaito cewar mutumin ya yiwa yaranyar mai shekaru uku dabara ne ya shigar da ita kango inda ya mata fyaden

- An ce mutumin ya yi amfani da hanunsa domin rufe mata baki yayin fyaden kuma hakan ya yi sanadiyar mutuwar ta

Yadda wani mutum a Katsina ya yiwa diyar makwabcinsa fyade, ya kuma kashe ta

Yadda wani mutum a Katsina ya yiwa diyar makwabcinsa fyade, ya kuma kashe ta
Source: Twitter

Ana zargin wani mutum mai shekaru 50 a duniya, Abdullahi Sani da yiwa diyar makwabcinsa mai shekaru fyade har ta kai ga ya halaka ta a garin Funtua da ke jihar Katsina.

Wanda ake tuhumar Abdullahi Sani da mahaifin yarinyar, Ibrahim Abdullahi duk mazauna Jabiri Quarters ne da ke Funtua.

An gurfanar da Sani a gaban Kotun Majistare da ke Katsina a ranar Alhamis inda ake zarginsa da aikata fyade da kisan wadda sun sabawa sashi na 283 da 221 na Penal Code.

DUBA WANNAN: Assha: Wani asararen mahaifi ya dirka wa diyarsa mai shekaru 13 ciki

Dan sanda mai shigar da kara ya shaidawa kotu cewar wanda ake zargin ya yiwa yarinyar dabara ya shigar da ita wani kango inda aka ce ya yi mata fyaden.

Sani ya yi amfani da hannunsa ya rufe bakin yarinyar a lokacin da ya ke aikata mummunar aikin wanda hakan ya sa ta rasu saboda rashin iya numfashi.

Dan sanda mai shigar da kara, Inspeckta Sani Ado, ya shaidawa kotu cewar sun kammala bincike amma duk da hakan ya bukaci kotun ta dage sauraran shari'ar zuwa wani rana nan gaba.

Alkali mai shari'a, Hajiya Fadile Dikko ta dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 20 ga watan Nuwamban 2018 amma ta bayar da umurnin a cigaba da tsare Sani a gidan yari har zuwa ranar sauraron shari'ar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel