Batan dabo a Filato: Muhimman bayanai 4 da baku sani ba game da rayuwar Janar Idris Alkali

Batan dabo a Filato: Muhimman bayanai 4 da baku sani ba game da rayuwar Janar Idris Alkali

Tun ranar 3 ga watan Satumbar da ya gabata ne dai iyalan Janar Idris Alkali suka bayar da sanarwar batan dabon da yayi bayan ya bar gidan sa a garin Abuja, babban birnin tarayya zuwa Bauchi.

Sai dai tun a lokacin kamar yadda matar sa ta bayyana basu kara jin duniyar sa ba tun dai bayan da suka yi wata ya kuma shaida mata cewa ya shiga garin Jos kuma yana ma niyyar fita.

Batan dabo a Filato: Muhimman bayanai 4 da baku sani ba game da rayuwar Janar Idris Alkali

Batan dabo a Filato: Muhimman bayanai 4 da baku sani ba game da rayuwar Janar Idris Alkali
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Neman Janar Alkali: Sojin Najeriya sun yi alkawarin kudi ga wanda ya bayyana shi

To sai dai bayan shafe kwanaki masu yawa, rundunar sojin Najeriya ta kafa wata bataliya ta musamman inda suka dora masu alhakin nemo jami'in nasu a raye ko a mace wadanda tuni suka soma aiki gadan-gadan.

Binciken sojojin dai kamar yadda muka samu ya dauki hankalin al'ummar kasa sosai bayan da aka gano motar Janar din a cikin wani kududdufi tare da wasu motocin 2.

Ga dai wasu daga cikin muhimman abubuwan da ya kamata ku sani game da Janar din:

1. Dan asalin jihar Yobe ne dake a shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya.

2. Janar Alkali ya shafe shekaru 35 yana aikin soja.

3. Ya yi ritaya a watan Yunin shekarar 2018.

4. Kafin ritayar sa, shi ne babban jami'in gudanarwa na rundunar sojin Najeriya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel