El-Rufai ya bayyana hanya daya tilo da Shehu Sani zai samu nasara a Kaduna

El-Rufai ya bayyana hanya daya tilo da Shehu Sani zai samu nasara a Kaduna

Gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa samun nasara a zaben fitar da gwani na jam’iyyar APC ga Sanata Shehu Sani ya tattara ne a hannun wakilan jam’iyyar da zasu kada kuri’a a zaben, ba a hannunsa ba.

Legit.ng ta ruwwaito El-Rufai ya bayyana haka ne a yayin da yake tattaunawa da yan jaridu jim kadan bayan fitowarsa daga ofishin shugaban kasa Muhammadu Buhari inda suka tattauna da shi game da matsalolin da ake samu a zaben.

KU KARANTA: Gwamnatin tarayya za ta jinginar da manyan tashohin sauka da tashin jiragen Najeriya

El-Rufai ya bayyana hanya daya tilo da Shehu Sani zai samu nasara a Kaduna

El-Rufai da Shehu Sani
Source: UGC

“Shugaba Buhari ya jaddada matsayinsa na cikakken dan siyasa, haka zalika bai taba goyon bayan ayi ma jama’a dauki dora ba, don haka ba matsalata bace, kuri’a daya ke gareni a zaben fitar da gwani, don haka ya rage ma wakilan jam’iyya su zabi Shehu Sani ko akasin haka, amma tsarin dimukradiyya shine a baiwa koma dama ya fafata a zabe.

“Kun san Shehu Sani yayi abubuwan da suka nuna baya tare da jama’an Kaduna, don haka yanzu lokaci ne da zai bayyana ma wakilan jam’iyya dalilin da yasa ya aikata abinda ya aikata.” Inji Gwamnan.

Daga karshe gwamnan jahar Kaduna ya bayyana tabbacinsa na cewa jam’iyyar APC za ta cimma ranar da hukumar INEC ya sanya na bukatar kowanne jam’iyya ta mika mata jerin sunayen yan takarkarunta.

Idan za’a tuna a satin daya gabata ne aka samu wata takarda dake dauke da sunayen yayan jam’iyyar APC da zasu fatata a zaben fidda gwani bayan jam’iyyar ta amince da takararsu, inda a jerin sunayen an samu sunan Shehu Sani shi kadai daga sanatoriyar Kaduna ta tsakiya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel