Dalilin da yasa muke tarwatsa Saraki, Dino, da sauran yan PDP da barkonon tsohuwa

Dalilin da yasa muke tarwatsa Saraki, Dino, da sauran yan PDP da barkonon tsohuwa

Hukumar yan sandan Najeriya ta bayyana dalilin da yasa ta watsawa shugabannin jam’iyyar Peoples Democratic Party PDP barkonon tsohuwa a zanga-zangar da suka gudanar a yau Juma’a, 5 ga watan Oktoba, 2018.

Hukumar ta bayyana cewa yan siyasan sun tayar da hankulan jama’a a cikin garin Abuja ta hanyar tare hanyoyi da hana jama’a wucewa na tsawon awanni.

Kakakin hukumar yan sandan, DCP Jimoh Moshood, ya bayyana hakan a wata doguwar jawabi da ya saki da yammacin nan a birnin tarayya Abuja.

Yace: “Sanata Bukola Saraki, Sanata Dino Melaye, da Sanata Ben Bruce sun fito idon duniya suna tayar da tarzoma, sun tara titin Shehu Shagari na awowi kuma hakan ya hana motoci da jama’an birnin tarayya.

Sun tayar da hankulan jama’a har suka kai farmaki ga jami’an yan sanda a hedkwatan hukumar inda suka fara ingiza jami’ai domin shiga ciki ofishin hukumar su yi lalata. Saboda haka muna gayyatansu ofishin hukumar ranan Litinin, 8 ga watan Oktoba, 2018 domin bincike.”

Duk da kalaman batanci da zage-zagen da sukeyi, babban jami’in yan sandan bai dau wani tsattsaurin mataki ba, innama ya umurci jami’ansa su tarwatsasu.”

KU KARANTA: Ilimi: Jerin darajar matsayi a makarantan Allo (Hotuna)

Mun kawo muku rahoton cewa Jami'an yan sandan Najeriya sun watsawa shugabannin jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP barkonon tsohuwa yayinda suke gudanar da zanga-zanga zuwa ofishin hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC a yau.

Daga cikin shugabannin jam'iyyar da suka tafi zanga-zangar sune shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki; gwamnan jihar Sokoto, AMinu Waziri Tambuwal; shugaban jam'iyyar PDP, Uche Secondus; dan takaran kujeran shugaban kasa, Sule Lamido da shugaban jami'ar Baze University, Datti Baba Ahmed.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel