Ranar Malamai: An mayar da malamai saniyar ware a Nigeria - Masu ruwa da tsaki

Ranar Malamai: An mayar da malamai saniyar ware a Nigeria - Masu ruwa da tsaki

- Ranar 5 ga watan Oktobar kowacce shekara ne ake gudanar bukin murnar 'Ranar malamai ta duniya'

- Masu ruwa da tsaki a fannin ilimi sun bayyana cewa an mayar malamai saniyar ware a cikin sauran ma'aikata

- Haka zalika sun gabatar da bukatar kara yawan shekarun ritar malamai zuwa shekaru 70

A yayinnda malamai a fadin duniyar ke bukin murnar zagayowar ranar malamai, wasu daga cikin masu ruwa da tsaki a harkokin ilimi sun shawarci gwamnatin Nigeria da ta dauki matakai wajen inga rayuwar malamai kasancewar an mayar da su saniyar ware a kowane ci gaba na ma'aikata.

Sun gabatar da wannan bukatar ne a jawabansu daban daban da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN a ranar Juma'a a jihar Legas.

Mr. Anslem Izuagie, shugaban makarantar sakandiren maza zalla ta Saint Johns da ke jihar Edo, ya bukaci gwamnatoci a matakai daban daban da su bunkasa walwalar malamansu fiye da na kowane ma'aikaci.

KARANTA WANNAN: Magidanci ya roki kotu ta warware aurensa da matarsa saboda gazawarta na biya masa bukata

Ranar Malamai: An mayar da malamai saniyar ware a Nigeria - Masu ruwa da tsaki

Ranar Malamai: An mayar da malamai saniyar ware a Nigeria - Masu ruwa da tsaki
Source: Depositphotos

Ya kawo bukatar samawa malamai wani tsarin albashi na musamman da kuma kara masu wa'adin shekarun yin ritaya zuwa shekaru 70 kamar yadda ake yi a jami'un kasar.

"Walwalar malaman kasar na da matukar amfani, ma damar dai ana son a bunkasa fannin ilimi da kuma tabbatar da dorewar ingancinsa. A halin yanzu zaka taras malamai na bin wasu gwamnonin bashin albashi na watanni," a cewar sa.

Mr Hamed Adeleke, daya daga cikin masu ruwa da tsaki a fannin ilimi, ya shawarci gwamnati da ta dauki horas da malamai akai-akai da muhimmanci don bunkasa iliminsu da kwarewa wajen koyar da dalibai.

Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel